A karshen makon da ya gabata ne aka bude gasar wasan kwallon kafa ta Abba Gida-Gida cup a filin wasan kwallon kafa dake harabar Gidan Talebijin na Abubakar Rimi dake Hotoro.
Gasar dai an shirya tane saboda ta ya mai girma gwamnan jihar Kano Injiya Abba Kabir Yusuf murnarcika shekara daya akan karagar mulkin jihar Kano da kuma murnar dinbin nasarori da ya samu.
Gasar wadda ta sami halartar manyan mutane da dama cikinsu harda kwamishinan yada labarai, Hon. Baba Halilu Dantiye an bude ta da wasa tsakanin karamar hukumar Kumbotso da takwararta ta Kura a inda Kumbotso ta sami nasara da ci daya mai ban haushi.
Hajia Hauwa Isa Ibrahim, zakakurar shugaban gidan talabiji na ARTV ce ta ta dauki nauyi gasar wadda zaa rinkayi mako mako a harabar ARTV din.
Cukin manyan bakin da suka halarci bude gasar akwai Abubakar Adamu Rano, MD Radio Kano da shugaban Barcelona na jihar Kano Alh Bala Abidoka da kuma manyan jami’an kananan hukumomi na jiha.
A wani labarin kuma, mujallar wasanni ta WAFIYYA HAUSA ta karrama MD ARTV, Hajiya Hauwa Isa Ibrahim da lambar yabo saboda yadda ta kawo canji da cigaba cikin kankanin lokaci da kuma mayar da gidan aiki awa 24.
Mujallar wasanni ta WAFIYYA HAUSA ta lura cewa Hajia Hauwa ta zama ta farko wajen maida ARTV tasha mai aiki ba dare ba rana kamar yadda saurar shahararrun gidajen yada labarai sukeyi a duniya.
Mai girma kwamishina Dantiye ne ya mika mata lambar yabon tare da da Alh Bala Abidoka.
Fatanmu Allah ya kara daukaka, amen.