Ba wani mahaluki a jahar Kano musamman a karamar hukumar Dala da zaifi Ali Nayara Mai Samba murna jiya Lahadi a lokacin da ya tara dubunnan matasa na cikin birni da kewaye a filin wasa na Kurna Babban Layi a wajen wasan karshe na Mai Samba Unity Cup 2025.
Ganin dandazon jamaar da suka taro a wajen wasanne yasa Mai Samba cikin farin ciki, da annashuwa wanda kuma ya sashi kasa zaune da kuma tsaye sai dai zirga zirga.
Hakika taro yayi taro domin Ali Nayara Mai Samba yayi kira kuma matasa sun amsa don ta ko’ina tuttudowa sukeyi duk da haduwar hadari, al’amarin da ya tsunduma Mai Samba cikin murna da faraa tun kafin a fara wasan har zuwa kammala shi.
Kasar wadda kungiyoyin kwallon kafa na ungowowi 28 suka shiga an shirya tane don ta ya maigirma gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru biyu akan karagar mulkin Kano da kuma ayyukan raya jiha da yake ta aiwatarwa.
Kungiyoyin unguwa ishirin da takwas din da suka fafata a kasar sun hada da Kurna. A,
Hotoro, Gwale, Gwammaja, Kawo, Kwankwaso, Tsakuwa , Kurna. C, Kofar Ruwa , Kofar Mata, K/Wai-Dwn, Bichi da kuma Miltara.
Sauran sun hada da Sabon Gari, Fagge, K/Nasarawa, Dorayi, Rijiyar Lemo. B, Alfindiki, Dala, Yakasai, Brighet, Gwammaja.B, Rijiyar Lemo. A, Bachirawa, Kurna. B, Goron Dutse da kuma Bakin Kasuwa.
A wasan karshen dai kungiyar unguwar Kurna C ce ta lallasa kungiyar unguwar Brighet da ci biyu da daya. A wasan neman na uku kuma kungiyar unguwar Mil Tara ce ta doke kungiyar Kurna. A da ci daya mai ban haushi.
A karshen wasan a bada lambobin yabo wanda aka fara bawa Mai Girma Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf
Wanda an mikawa wakilin Gwamnan lambar yabonne don ayyuka tukuru da kuma kokarinsa na wanzan da zaman lafiya da kuma hana shaye shaye da kwacen waya da kuma ciyarda wasannin gaba a jihar Kano.
Mutum na biyu da aka karrama da lambar yabo shine Hon. Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano. Wanda aka karramashi don kokarinsa na bunkasa matasa da kuma wasanni a ko’ina cikin yankin jihar nan.
Ogan boye, shugaban karamar hukumar Nasarawa ma an karramashi saboda zama shugaba na gari don nasarorin da yake samu a mulkinsa da kuma ci gaban matasan Kwankwasiyya.
Suraj Imam, shugaban karamar hukumar Dala ma an karramashi da lambar iya kyakkyawan shugabanci da kuma kokarinsa na cigabn jamaar karamar hukumar Dala.
Haka kuma an karrama Sani Danja don kokarinsa na cigaban matasa a jihar Kano.
Sabon Janaral Manaja na kungiyar Kano Pillars ma watau Ahmed Musa (M.O.N) an karramashi da lambar kokari wajen cigaban al’umma musamman a bangaren wasanni da kuma tallafawa gajiyayyu.
Dan wasa Rabiu Ali Fagge ma an karramashi don zama fitatcen dan wasa a gasar Nayara Sallah Competition da kuma kokarinsa a wasan premier ta kasa.
Haka kuma Shehu Abdullahi ma ya karbi lambar yabo wajen kokarinsa na koyawa matasa wasa da kuma yin aiki tukuru.
An kuma raba kyaututtuka ga yan wasan da sukayi shura a garsar wanda Auwal Ali Malan dan wasan Kurna A wanda yafi kowa jefa kwallaye a raga ya lashe da cin kwallo shida.
Naziru Auwalu dan wasan kungiyar Kurna C da Ladan Muhd na kungiyar Tsakuwa sune suka lashe kyautar kwararrun yan wasan gasar watau Best young players of the tournament.
Haka kuma dan wasa Muhd Ahmad na kungiyar Miltara ne mai tsaron gidan da yayi fice a gasar watau Best Goalkeeper.
Fahad Usman na kungiyar Brighet ne ya lashe kyautar dan wasan da yafi tausayi watau Fair play player of the tournament.
Sani Zidan na kungiyar Miltara shine ya zama kocin da yafi fice watau Best Coach of the tournament.
Kungiyar Brighet it ace ta zama kungiyar da tafi kowacce watau Best Team. Su kuma kungiyar Hotoro sune suka zama wadanda sukafi kowa da’a watau Most discipline Team.
Da yake magana da wannan kafa, Ali Nayara Mai Samba wanda kuma shine shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ya bayyana godiyarsa ga dimbin jamaar da suka halarci wajen waccan gasar da kuma musu fatan alheri.
Ya kuma sheda mana cewa ya yanke shawarar shirya gasarne don ta ya mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru biyu akan garagar mulkin jihar Kano.
Mai Samba ya kuma godewa mai girma gwamna saboda irin ayyukan alheri da yake ta aiwatarwa a fadin yakin jihar Kano.
Ya kuma yi adduar kara samun nasarori akan wadanda ake samu.