Tun lokacin da sirrin zargin kulunboton da aka yiwa Kano Pillars ya fito wanda kuma mutane da dama suke alakantashi da rashin nasarasu a kakar wasan kwallo kafa ta bana, nake ta addu’ar ka da Kano Pillars su sa wancen kulunboto a zuciya.
Domin sa kulunboton a zuciyarsu ba karamin hatsari da illa bane domin karya zuciyarsu gaba daya zaiyi kuma abu ya kara tabarbarewa.
Domin shugabannin da yan wasan duk za suyi La’asar, jikinsu yayi sanyi su kasa tabuka komai saboda sa wancen kulunboto a zuciya. Su tuna Hausawa na cewa, “Shi tsafi gaskiyar mai shi ne”.
Inason dukkaninsu su cigaba da addu’o’in da suka saba kuma, su kuma kara kaimi don cigaba da samun nasararori kamar yadda suka murkushe yaran Ikorodu.
Kamar yadda na zayyana a cikin rubuttukana a baya, tunda Allah yasa kungiyar Barau sun samo bakin zaren nasara, haka nake fata Kano Pillars ma ta samo nata bakin zaren.
Nasan mutane da dama na yiwa kungiyar kwallon kafa ta Pillars addu’a da fatan samun nasara, to sai su dage don hakan ta tabbata.
Ina kuma fatan tun yanzu shugabannin kungiyar da hadin kan mai horaswarsu sun san irin yan wasan da suke nema don cike gurbi idan an bude kofar yin rijistar sababbin yan wasa.
Yakamata kuma su fara tuntubar yan wasan da kuma kungiyoyin da suke nema don sanin ko zasu zo kokuma a’a.
Su tuna kawo kwararrun yan wasa na bukatar hadin kan gwamnati domin abune wanda zai gabtari kudi masu yawan gaske.
Saboda yadda yan wasan zasu bukaci kudi masu kauri kafin dawowarsu haka kungiyoyinsu zasuyi kafin amincewarsu komowa Kano Pillars.
Ina kuma kara tunawa shugabannin Kano Pillars cewa wasan kwallon kafa a wannan kasar baa fili kawai akeyinsa ba.
