Kamar yadda mutanen da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf suke ta igiraren cewa kungiyar ba kudi ba kudi, nabi sahun dan jaridar gidan rediyou Nasara, Wasilu Kawo cewa to su sauka tunda abin ba dole bane.
A cewarsa fadin ba kudi ba kudi da mahukuntan da aka dorawa alhakin gudanar da tafiyar da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars nemawa gwamnatti bakin jini ne kawai ba wani abu ba.
Kamar yadda Kawo ya wallafa a shafinsa na Facebook, cewa, so kawai ake a dorawa gwamnati laifi don tayi bakin jini ba wani abu ba.
Hakika nima nabi sahun Wasilu Kawo wajen fadin hakan tunda sunce baa basu kudin gudanar da kungiyarba to su sauka don nuna takaicin hakan.
Sai sun ajiye aikinne zamu tabbatarr da ikirarin da sukeyi.
Ko kuma ita gwamnatin ta hukunta su in ta san ta ba su suke cewa ba’a basu ba.