Hakika dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta cikin Birnin Kano watau (Kano Municipal), Hon. Sagir Ibrahim Koki ya dara sa’a a cikin tsarayensa ko takororinsa na Abuja masu wakiltar mazabobi dabam dabam dake jihar Kano.

Jajircewarsa wajen halartar zama da ayyukan majalisar wakilai yasashi samarda wakilci nagari a majalisar wanda yasa shi yin fice wajen yin abinda ya jeyi a majalisar wakilai ta Abuja Abuja.

Rashin zamansa kurma ko bebe a majalisar yasa shi to fa albarkacin bakinsa a dukkannin mahawarorin da akeyi a majalisar.

Koda wajen ayyukan kwamitocin majalisa, baabarshi a bayaba domin babu wanda bai halarta indai bai fita waje wajen wani aikin ba.

Zamansa wakili a majalisa ya amfanawa jamaa da dama domin ya samawa dukkannin mazabu goma sha uku (13) dake cikin yankin mazabar tarayyar da yake wakilta.

Don ragewa dimbin jamaar mazabarsa radadin yanayin matsin tattalain arziki da ake ciki, Hon Sagir ya samar da shinkafa buhu 4,400 ga yan jam’iyyarsa to NNPP da kuma da kuma tallafin kudi Naira Miliyan sittin (N60m) a garesu.

A fannin lafiya kuwa, Hon. Sagir Ibrahim ya dauki nauyin aikin gyaran idanun mutum 2000 na dukkan  mazabu goma sha uku 13 inda wasu duba idanun nasu akayi aka kuma basu magani kawai. Wasu kuwa gilasai aka basu bayan kamala duba idanunsu. Sauran kuwa aiki akayi musu a idanuwan nasu don samun gani kamar yadda suke ada.

Don samarda ruwansha a wajajen da ake rashinsa sosai, Hon. Sagir ya kasa aikin tonon rijiyoyin birtsatse kasha-kashi.

An kuma sami nasarar kammala kashin farko na tonon rijiyoyin birtsatse a mazabu goma sha uku na mazabarsa ta tarayya.

Hon Sagir ya kuma bada umarni don shiga kash na biyu a inda aka tona wasu rijiyoyin a mazabun Tudin Wazirci, Zango da kuma Dan Agundi.

A kashi na uku kuwa, Hon. Sagir ya bada umarnin ginin rijiyoyi a mazabar Zaitawa, Daganda, Koki Lungun Makaranta, Chedi, Jakara da Sharada.

Hon Sagir ya cigaba da gina rijiyoyinne a lunguna da sakoki don samawa jamaa tsabtataccen ruwan da za suyi amfanin gida da shi.

A bangaren samarda tsaro da walwalar jamaa kuwa, Hon. Sagir Ibrahim Koki ya samarda fitilun masu aiki da hasken rana wato (Solar) 1,300 a mazabu goma sha uku na mazabar tarayya ta Kano Municipal.

A farnin ilmi ma Hon. Sagir yana aiki sosai domin yana gina ajujuwa shida a makarantar Maryam Aloma dake mazabar Kankarofi.  Yana kuma gina wasu ajujuwa tara a mazabar Sharada.

A wajen gyaran makarantu kuwa, Hon. Sagir nan ma yayi fice domin ya gyara su da dama da kuma gyaran kananan cibiyojin lafiya na fadin yankin mazabunsa. A cikinsu akwai makarantar Laurat Ibrahim Shehu dake Koki.

Hon Sagir ya kuma samarda wajen zama da rubutu (Desks and Benches) masu yawan gaske don samun natsuwar yara a makarantu a lokutan daukar darasa.

Hon. Sagir kuma yana daukar nauyin dalibai masu karatu mai zurfi da kuma tallafawa wasu daliban da abinda ya samu don gudanar da karatunsu a saukake.

Haka kuma yana daukar nauyin koyawa matasa da mata aikinyi da kuma bada tallafin yin sana’o’in da aka koya musa.

Hon. Sagir ya kuma dauki nauyin koyawa matasa masu yawa koyon gyaran waya da kuma basu kayan aikin gyaran.

A bangaren ginin tituna kuwa, shima Hon. Sagir yayi rawar gani inda ya shimfida kwalta a tituna goma sha takwas cikinsu harda titin Kundila Gandu, Alkali Rabo da kuma Kurma. Haka kuma an kammala gina titin Kofar Wambai zuwa koki (Mayanka), sharada da Tukuntawa

A bangaren kwalbati kuwa, Hon. Sagir ya bada umarnin sake ginin magunanan ruwa dabam dam a fadin mazabarsa don kaucewa ambaliyar ruwa lokacin damina.

Bayan samun labarin lalata na’urorin samarda wuta (transformer) da wasu bata gari keyi, Hon Sagir ya duki nauyin gyaransu a Bakin Zuwo, Koki, Malam Ganari, Yan Awaki da Zaitawa nan take da kuma kasha makudan kudi don killacesu don kariya nan gaba.

Haka kuma, Hon. Sagir ya samawa matasa aikinyi a maaikatun gwamnatin tarayya da dama da kuma tallafawa wadanda suka sami shiga aikin yan sanda.

Jamaar da muka zanta dasu sunyi murna da ayyukan raya kasa da Hon Sagir yake yi musu da kuma adduar samun nasarori anan gaba.

Haka kuma mutane dabam dabam da kuma cibiyoyi ne suka girmama Hon. Sagir Ibrahim Koki da lambobin yabao dana girmamawa.

Allah kara daukaka.

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.