Khalifa Bashir Sheikh Musa Kallah na mika godiyarsa da kuma ban gajiya amadadin iyalai da kuma dukkanin almajiran zawiyyarsa ga darirruwan jama’a da suka halarcci daurinauren dan sa.
Daurin auren wanda aka gabatar a masallacin Alfukan, anyi shine ranar Jumaar da ta gabata bayan sallar Jumaa.

Mutane da dama daga farni farni na rayuwar al’umma suka halarci wajen daurin auren kuma suka sa albarka.
Ko shakka babu anga taron mutanen kasashen waje, mayan malamai, manyan yan boko, manyan yan siyasa da kuma jami’en tsaro da kuma darirruwan mutane a wajen dauren auren.

Anga halartar dukkanin mambobin majilasar Shura na Darikar Attijaniya, wakilan ofisoshin jakadanci na kasashen Sudan, Niger, Lebanon da Tunis a wajen daurin auren. Haka kuma akwai manyan yan kasuwa, manyan malamai da kum yan siyasa.

Babu tambaya, daga ganin fuskar uban ango, Khalifa Bashir Sheikh Musa Kallah, kasan tana cike da farin ciki wanda ba zai zaiyanuba domin bakinsa a bude yake saboda murnar ganin tururruwar dan adam da suka amsa gayyatarsa.
Fatanmu Allah yasa albarka.