Hakika gwamnati a cikin rayuwa da harkokin jama’arta yar kallo ce. Sai da babban aikinta shine sa ido da kuma samar da tsarirrika da yanayi wanda jama’arta zasu sami damar tafiyar da harkokinsu a sauwake cikin lumana.
Gwamnatoci na samun kwanciyar hankali da kuma gudanar da mulkinsu a saukake, idan sun fuskanci jama’arsu na da abinyi kuma harkokinsu na wanzuwa ko tafiya daidai ba cuta ba kuma cutarwa.
Kowa ya sani ba aikin gwamnati bani shiga harkokin kasuwanci ko makamancinsu, a’a, aikin gwamnati shine samarda da yanayin yin kasuwancin ko wasu muhimman harkoki na halas da kuma tsaro dan komi ya tafi daidai.
Amma yana zama wajibi a wasu lokutan gwamnati ta tsunduma kanta cinki harka musamman idan ta duba cewa jama’arta na da shaawa ko muradin wannan harka amma babu masu gudanarwa ko zuba jari a cikinta.
Irin wannan dalilinne yasa gwamnatocin kasar nan da dama ke tsuduma cikin harkar mallakar kungoyin wasanni kamar kwallon kafa, kwallon kwando, kwallon raga da sauransu.
Alal misali a Maiduguri gwamnatin jihar Borno ke daukar nauyin kungiyar kwallon kafa ta El-Kanemi, a jihar Pilato, gwamnatin jihar ke da Plateau United, a jihar Kwara, akwai Kwara United, a jihar Rivers, gwamnatin jiharce ke daukar nauyi Rivers United, sai nan Kano inda gwamnatin jihar Kano ceke daukar nauyin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars haka kuma sauran jahohi.
Gwamnatocin jahohi na daukar nauyin wadannan kungiyoyin wasanne saboda rashin samun shigar yan kasuwa ko kungiyoyin da ba na gwamnati ba shiga harkar saboda makudan kudin da harkar ke ci sannan kuma babu wata tabbatacciyar riba a ciki.
Da akwaimasu daukar nauyin irin wadaannan kungiyoyi, to fa babu yadda gwamnatocin jihohi zasu tsunduma kansu cikin harkar, saidai kallo kawai.
Don haka tunda a yanzu a Kano an sami mutane daidaiku suna nuna shaawarsu wajen daukan nauyin ko mallakar kungiyoyin wasan kwallon kafa a jihar Kano, to fa zama wajibi ga gwamnatin jiha to fito fili ta taimakawa kungiyoyin don samun nasararsu.
Wajibcin hakan ya faru ne saboda damar da yawacin matasan jiharnan suka samu na damar yin wasan a kungiyar Barau ba tare da sun je ko’ina ba.
Bugu da kari jama’ar gari ma sun sami wata damar na kasha kwarkwatar idanunsu wajen ganin manya kungiyoyin wasan kwallon kafa na wasu jahohi.
A halin yanzu, matsayin kungiyoyinmu biyu masu daraja, watau Kano Pillars FC da Barau FC dake cikin gasar Nigeria Premier Football League (NPFL) sun zama abin damuwa ga masoya, ‘yan wasa da masu ruwa da tsaki a harkar wasanni a fadin Jihar Kano da ma kasa baki daya.
Wadannan kungiyoyi biyu, wadanda a da suke alfahari da daukaka ga jama’ar Kano, yanzu suna fama da rashin nasara tare da kasancewa a kasan teburin gasar, lamarin da ke bukatar gaggawar kulawa daga gwamnati.
A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa Barau FC na da maki biyar kacal, yayin da Kano Pillars FC ke da hudu, abin da ke nuni da tabarbarewar da ta samo asali daga rashin kyakkyawar tafiyar da al’amuran gudanarwa da kuma matsalolin fasaha.
Magoya baya sun dade suna jimami da takaici yayin da suke kallon kungiyoyinsu nata rashin nasara a gasar duk da tarihin Kano na kasancewa cibiyar hazikan ‘yan wasa da kwarewa a harkar kwallon kafa.
Bincike da lura sun nuna cewa akwai wasu muhimman dalilai da suka haddasa wannan tabarbarewowin:
- Rashin Kyakkyawar Gudanarwa: Babu isasshen kulawa da tsari tsakanin shugabancin kungiyoyin da hukumomin gwamnati masu kula da harkar wasanni.
- Rashin Kudi da Tsarin Amfani da Albarkatu: Kungiyoyin suna fama da karancin kudi ko kuma rashin tsari wajen kashe kudade, da kuma matsalar kulawa da ‘yan wasa, wanda ke rage musu kwarin gwiwa.
- Matsalar Koyarwa da Horarwa: Sauyawa a fannin masu horarwa da rashin tsayayyen tsarin fasaha suna hana kafa daidaitaccen tsari na dogon lokaci.
- Rashin Zuba Jari a Matasa: An kasa baiwa matasa dama ta shiga cikin kungiyoyi ta hanyar horarwa daga matakin ƙasa, lamarin da ke sa kungiyoyi su dogara da siyan ‘yan wasa na wucin gadi.
- Rashin Tsari da Binciken Ayyuka: Rashin bin diddigin aikace-aikace da rashin gaskiya a cikin tsarin gudanarwa ya jawo watsi da nagarta da sakaci.
Don dawo da martaba da nasarar kungiyoyin, ina bada wadannan shawarwarin ga Gwamnatin Jihar Kano da masu ruwa da tsaki:
- Kafa Kwamitin Bincike Mai ‘Yanci: Gwamnati ta nada kwamitin kwararru da tsofaffin ‘yan wasa, masu gudanarwa, da wakilan magoya baya domin yin cikakken bincike kan yadda ake tafiyar da Pillars da Barau FC.
- Yi Binciken Kudi da Gudanarwa: A gudanar da cikakken binciken kudade da tsarin gudanarwa domin gano kura-kurai da daukar matakin gyara.
- Tsarin Sabon Gudanarwa: A kafa sabon tsari na gudanarwa wanda zai kasance mai zaman kansa amma na gaskiya da amana, tare da sakamako bisa aiki da nagarta.
- Zuba Jari a Matasa da Harkar Gargajiya: A farfado da kungiyoyin matasa da cibiyoyin horaswa domin samar da sabbin ‘yan wasa masu kwarewa daga Kano da kewaye.
- Kafa Shugabannin Fasaha Masu Kwarewa: A nada koci da jami’an fasaha masu kwarewa tare da tabbatar da suna da kwangila da sharuddan aiki bisa nasarori.
- Gwamnati Ta Kara Kula da Bin Didddigi: Duk da karfafa hadin gwiwar masu zaman kansu, gwamnati ta ci gaba da sa ido don tabbatar da cewa duk kudade da kayan aiki suna zuwa ga manufar ci gaban kungiyoyin.
Martabar Kano a fagen kwallon kafa tana cikin barazana saboda irin wannan tabarbarewa.
Lokaci ya yi da Gwamnatin Kano ta dauki mataki cikin gaggawa domin dawo da karfin gwiwa, kwarjini, da sahihancin gudanarwa a Kano Pillars FC da Barau FC.
Idan aka dauki matakai cikin hikima yanzu, wadannan kungiyoyi za su sake zama tushen farin ciki, hadin kai da ci gaban tattalin arziki ga al’ummar Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Haka kuma yakamata gwamnati ta sani cewa barin su wadannan kungiyoyin a haka babbar illace ga jihar Kano a fagen wasan kwallon kafa.
A fidda siyasa, a kuma duba jihar Kano da kuma cigaban jihar kawai.