Shekaran jiya, ɗaya daga cikin masu bibiyar rubuce-rubucena ya ziyarce ni har gida, ya kuma ba ni wani labari mai cike da ruɗani da ban mamaki.
Labarin ya shafi dalili da ake zargin shi ne ke haifar da raguwar ƙoƙari da kuma rashin samun sakamako mai gamsarwa da ƙungiyar Kano Pillars ke fuskanta a wannan kakar wasa ta bana.
Da ya kammala ba ni cikakken labarin da yake ikirarin shi ne babban dalilin da ya sa Kano Pillars ke ta fama da gazawa a wannan lokacin, sai ya gane a fili cewa ban ɗauki maganarsa da wani nauyi ba.
Duk yadda ya dage yana jaddada cewa labarin gaskiya ne kuma ya tabbatar da sahihancinsa, har wani ban nuna alamar amincewa da abin da yake faɗa ba.
Wannan rashin gasgatawa ta fuskar da na nuna ya sa ya fahimci cewa lamarin yana buƙaci ƙarin hujjoji kafin ya samu na yarda.
Wannan tasashi turomin wani fefan vidiyo a (whatsapp) wanda wani ma’aikacin Radio Arewa ya wallafa dan gane da wani labari da wani mutum ya zo har gidan radiyonsu ya sheda masa.
Hakika, akwai abubuwa da dama masu cike da mamaki da ruɗani da na gani a cikin wancen fefan, waɗanda a zahiri ba abin mamaki bane idan aka ga sun faru a cikin al’ummarmu.
Abubuwan sun yi kama da irin halaye da al’amuran da muka saba gani ko ji a tsakanin mutanenmu, don haka ba su zo min da wani sabon yanayi ba sai dai ƙarin tunani da nazari.
Kowa ya san cewa a cikin mutanenmu akwai wasu mutane masu neman duniya ta ko wane hali, wadanda babu tsoron Allah a zukatansu kuma za su iyayin komai don biyan bukatun nasu.
Irin waɗannan mutane kan iya aikata duk abin da ya zo musu a rai domin su cimma burin da suka sa a gaba, ba tare da yin tunanin illar da hakan zai iya haifar wa kansu ko al’umma ba.
Ba sa tsoron ko tunanin abin da zai biyo bayan rayuwa ta lahira, domin zuciyarsu ta riga ta rufe da son abin duniya ko ta wane hali.
Zasu iya aikata kome, ko da kuwa abin yana da muni ko tasiri mara kyau muddin ko idan dai sun yi imanin cewa hakan ne zai cika musu burin da suka sa a gaba.
To amma, kamar yadda ake cewa, wani hanzari ba gudu ba. Dole ne mutum ya tsaya ya tambayi kansa: Menene ainihin dalilin da yasa aka yi wannan kulunboton, kuma menene tasirin aikatashi ga kungiyar Kano Pillars?
Bugu da ƙari, abin da ya fi jan hankalina shine, ta yaya wannan mutumin da ya tona asirin ya gano cewa an aikata wannan abin?
Shin akwai wani sahihin hujja da ya dogara da ita wadda ta nuna yadda akayi kulunboton ko kuma su wanene sukayi shi?
Duk waɗannan tambayoyi suna buƙatar zurfin tunani da gamsassun amsoshi kafin a yadda da wannan labarin.
Tunda farko dukkanmu mun san cewa Kano Pillars a bana, ba ta yi cikakkiyar shiri ba don fuskanta ko tunkarar abubuwan dake gabanta.
Rikicin da ya biyo bayan rabuwa tsakaninta da tsohon mai horaswarta Usman Abdalla ya dagula tsarin kungiyar, musamman ganin cewa ba su gaggauta samo sabon mai horarwa ba.
Wannan gibi da aka samu ya shafi daidaiton ‘yan wasa, ya rage karsashin atisayen su, kuma ya jawo tangardar shirye-shiryen da ya kamata su yi kafin fara sabuwar kakar.
Saboda haka, rashin tsari da wuri-wurin don warware matsalolin horarwa ya taka muhimmiyar rawa wajen raunana kungiyar a wasan farko-farko na kakar.
Wannan yasa shugabannin kungiyar korar mai horaswar kungiyar da mataimakinsa bayan was an kungiyar da ta Barau.
Kada mu manta cewa a wannan kakar, Kano Pillars ba ta dauko nagartattun ‘yan wasa ba domin cike gibi bayan fitar wasu yan wasan su zuwa kungiyoyin.
A fili yake rashin maye gurbin wadannan muhimman ‘yan wasa na bangarori daban-daban ya kara dagula tsarin kungiyar.
Hakan ya janyo raguwar karfi da gogewa a wasu sassa na kungiyar, musamman wajen da ake bukatar jarumai masu iya jan ragamar wasa.
A ganina wannan kuskuren rashin dauko sababbin kwararru yan wasa ya kasance daya daga cikin manyan abubuwan da suka hana Pillars samun daidaito da karsashi tun farkon kakar ba tsafi ba.
Haka kuma, cunkushe fannin gudanarwa na kungiyar da gwamnati ta yi da mutane masu yawa wadanda yawancinsu ba su da isasshen masaniya game da harkokin kwallon kafa musamman (Premier League) ya kara jefa Kano Pillars cikin rudani.
Ga kuma yawan shisshigi daga yan kallo ko magoya baya wadanda ba su kware wajen tafiyar da kulob ba shima ya haifar da rashin daidaito, rikice-rikicen ra’ayi, da yanke shawara marasa tsari.
Wannan dabi’a ta tozarta tsarin shugabanci na kungiyar kuma ta kawo tangarda wajen aiwatar da ingantattun manufofi, ta kuma raunana tsarin aiki, sannan ta rage ikon masu horaswar kungiyar wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba tsafi ba.
A takaice, yawan mutane marasa kwarewa da aka zuba kan al’amuran kulob din ya kara jawo wa Pillars matsaloli fiye da mafita ba tsafi ba.
Ban ce tsafi bashi da tasiri ba, amma yana da kyau a sake nazari da tunani cikin hankali. A ganina, ba wannan kulunboton bane ya hana Kano Pillars cimma wani babban nasara a fili ba.
Matsalolin da suka addabi kungiyar sun fi danganta ne da rashin shiri mai kyau, rashin kwarewa a harkar gudanarwa, da rashin cikakken tallafi ga ‘yan wasa da horarwa.
A takaice, dalilan da suka hana Pillars tagaza abin da ya dace su ne na ainihi na cikin gida, ba wani abu mai sihiri ko tsafi ba.
A hakikanin gaskiya, babban kuskuren da aka tafka shi ne rashin nemowa kungiyar kwararrun ‘yan wasa da kuma gogaggen mai horaswa tun kafin a fara gasar.
Kuma idan mahukuntan Kano Pillars sukayi kuskuren tasirantar da tsafin da akace anyi musu don rashin nasararsu to an sami matsalar da baza a iya warkarwa ba.
Babbar matsalar shine rashin samo kwarrarun yan wasa domin da farko sun yi tunanin cewa wadanda suke da su za su iya wani abin a zo again a sabuwar kakar wasa, alhali ana bukatar karin karfi, sabbin dabaru, da sabbin fuska masu kwarewa don karawa kungiyar kuzari da karsashi.
Dogaro ga tsofaffin ‘yan wasa sam ba su wadatar ba shiyasa ko kuma ya tsunduma Pillars cikin rauni, ba tare da cikakken shiri ko karfin gwiwa ba tsafi ba.
A takaice, rashin daukar mataki da wuri wajen karfafa kungiya shi ne ya janyo matsalolin da ake gani yanzu ba tsafi ba.
Sam bana fata su Ali Nayara Mai Samba su yarda da tasirin wancen kulunboto akan halinda Pillars ke ciki, su nemi kwarrarun yan wasa idan an bude daukar yan wasan don karawa kungiyar karfi da karsashi.
Wannan raayina kenan.
Allah ya bamu saa, ameen
