Anyi kira ga mahukuntan jihar nan musamman gwamnan jihar Kaano Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya ceto kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars daga halin ni yasun da ta sami kanta a ciki a wannan kakar wasan ta bana.
Tsohon dan wasan Kano Pillars wanda kuma shine kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya watau Super Eagles ne yayi wannan kiran da yake zantawa da shugaban sashin wasanni na Radio Nasara, Muuhammadu Wasilu Kawo bayan kamala gasar Ramadan Cup da akayi a nan Kano.
A cewarsa arewa gaba dayanta ba Kano kawai ba na alfahari da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars don haka ya jawo hankalin mahukuntan jihar Kano da suyi abinda ya kamata don ceto Kano Pillars.
“A gaskiya raina yabaci kwarai da gaske dana ga halin da tsohuwar kungiyata ta Kano Pillars take ciki a wannan kakar wasan ta wannan shekarar, “ Ahmed Musa ya bayyana.
“Ina kira ga duk wanda yake da hannu yasa don a ceto Kano Pillars’’, Ahmed Musa ya kamala.
Idan baa mantaba Kungiyar Kano Pillars na ta samun matsaloli a wasanninta musamman na gabatowar azumi da na cikin azumi saboda rashin sirka yan wasan da suka dauka a farkon kakar wasannin bana.
Anan zanyi kaira da idan irin wannan lokacin ya sake dawowa to ayi hattara.
Ita kwallon kafa bakuwace baa yinta da yan kasa zalla, sai da sirkawa.