Ba wani boyayyen abu ko labari bane cewa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na cikin wani mawuyacin hali wanda kuma ya zama dole mushaidawa mai girma gwamna Abba Kabir Yusif don kawo agajin gaggawa.

Mawuyacin halin da kungiyar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars din ta fada ya samu ne saboda tsananin karancin kudi da kungiyar ke ciki.

Bincike ya nuna cewa maaikatar wasanni na yiwa kungiyar kanshin mutuwa saboda hanata kudin da ya kamata ta bata don gudanar da ayyukanta.

Mun kuma gano cewa duk wasan da kungiyar zatayi sai ta je maaikatar wasanni tana ta rara gefe da dan wuya kafin ta samu, al’amarin da masana wasanni ke Allah wadai dashi.

A yanzu haka da nake wannan rubutun (9.45 na safe) yan wasan kungiyar da masu horar da su na harabar Kano State Sports Commission akan titin Sani Mashal suna jiran samun kudin tafiya zuwa Port Harcourt ta jihar Rivers don yin wasansu da masu masaukinsu watau kungiyar kwallon kafa ta Rivers United.

Wanda Kano Pillars na bukatar zuwa da wuri don su huta domin kowa yasan wasane mai zafi da wahalar gaske musamman a wannan lokacin.

Ina kira ga gwamnati da su dubi Allah su kawo kashen wannan azabar da yan wasa, masu horarwa da shugabannin kungiyar Kano Pillars kesha.

Hana kungiyar issassun kudi a wannan lokacin tamkar zubarda damar cin kofin NPFL ne fa. Kuma zai iya rusa dukkannin kokarin da kungiyar tayi a abaya.

Bincike ya nuna kungiyar Kano Pillars ta ci bashi iya wuya na miliyoyin kudi don tafida al’amuranta amma har yau gwamnati bata basu kudi an biya ba, abinda yasa mutane ke jin tsoron kara musu wani bashin.

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.