Duk da yake har yanzu ban ga wata takardardar da ta baiyana sunayen wadanda shugabancin kungiyar Kano Pillars ta nada don bincikin mai horar da yan wasan kungiyar ba, dole nayi kira da ayi abinda yakamata.
Rohotanni dake yawo a gari na nuna cewa wani ko kuma wasu daga cikin yan kwamitin gudanarwar kungiyar wanda kuma ake alakantashi ko su da shugaban kungiyar saboda amincin dake tsakanisu aka nada don yin binciken da kuma mika rahotonsu nan da wata daya.
Hakika idan hakan ta tabbata, to an tabka kuskure wanda kuma bazai bari a sami sahihin sakammako ba wanda zaisa yin dana sani nan gaba.
Masana na cewa idan ana neman sahihin sakammako, to dole ayi abinda yakamata don kaucewa zargi da rashin amincewar rahoton.
Jamaa da dama na ganin cewa idan da gaske ake, to sahihen mutane zaa samo wadanda kuma yan baruwanmune masu mutunci da kima a dorawa wannan aikin.
A Kano muna da farfesoshi akan wasanni, alkalai (judges, magistrates) da sauransu masu harkar wassani su yakamata a zakulo a bawa aikin ba dan cikin gida ba.
Mu sani, yadda Babangida Little da sauransu ke tunkahon cikakkun yayan jihar Kano ne, haka Abdu Maikaba ke tunkahon shima dan jihar Kano ne.
Ko ba don hakanba, adalci abune mai kyau da mahimmanci a tsakanin jamaa. Don rashinsa babbar masiface da asarace ga al’umma.
A ganina a jami’o’in Bayero, Saadatu Rimi, FCE da maaikatar ilmi, sharia da sauransu akwai amittatun mutanen da zasu iya wannan aiki ba gudu ba tsoro.
Mu tuna fa sai munyi daidai za muga daidai.