Daruruwan mutane daga farni dabam-dabam na rayuwa da al’ummar kasarnan ne suka halarci daurin auren shahararren dan jaridar nan mai farin jini wanda yake aiki a Gidan Radio Nasara mai suna Muhammadudu Wasilu Kawo da amaryarsa Malama Aisha Usman.
Daurin auren wanda akayi Masallacin Da’awa na marigayi Sheikh Aminuddeen dake Sulaiman Crescent an daurashi da misalin karfe goma sha daya na ranar Lahadin da ta gabata.
Haka kuma yan jarida, yan siyasa, yan wasa da masu goya musu baya da sauran al’umma dayawa sukasami halartarr daurin auren da adduar albarka, zaman lafiya da samun zuriya dayyaba.
Cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren sun hada da tsohon shugaban Gidan Radiyo Kano da kuma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Alhaji Garba Bello Kankarofi, SSA na gwamna kan cigaban kasuwanci, Alh Abubakar Yahuza Gama, dan kwamitin gudanarwa Kano Pillars, Alh Naziru Wapa, shugaban kungiyar marubuta wasanni ta jihar Kano, Malam Zaharadden Saleh, tsohon shugaban kungiyar magoya bayan Kano Pillars Alhaji Bashir Muazu aka Bashir Jide da tsohon shugaban sashen labarai na KanoPillars, Lurwanu Malikawa.
Sauran sun hada da Tsohon daraktan wasanni na jihar Kano, Dokta Bashir Maizare,
Shugaban kungiyar Barca Kano, Alh Bala Abidoka, shugaban madrid na jahohin arewa sha tara, Alh Yusif Dankaka Dorayi da kuma Alh Nasiru Hamada PRO Real Madrid.
Haka kuma mataimakin manaja na Radiyo Nasara, Engr Muhammad Inuwa Jika shima ya halarta. Akwai kuma Shariff Zahradden Jadda, sabon shugaban sashen yan jaridu na Kano Pillars, shahararren dan jarid AA Tukko da sauransu.
Wasilu Kawo, wandake da dimbin magoya baya da masu sauraren shirirrikansa musamman na labarin wasanni ya nuna farin cikinsa ga dukkanin wadanda suka zo da kuma wadanda ma basu ssami damar zuwa ba. Ya kuma yi musu adduar Allah ya saka da alheri da kuma maidasu gida lafiya.
Kawo dai matashin dan jaridada mai hazaka da faran-faran da jamaa ya kuma godiwa dukkannin wadanda suka zo da duk wadanda basu zo ba.
Muna masa adduar Allah ya bashi yadda zayyi da kuma dawwamenmen zaman lafiya ameen.
Tuni Ango Wasilu ya tare a gidan amaryarsa.