Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      Gasar Kofin murnar cika shekara biyun Gwamna Abba: Mai Samba yayi hamdala

      July 28, 2025

      New coach for Pillars this week? Mai Samba confirms

      July 23, 2025

      FISU Games: Prof Yakasai showers admiration on Dikko

      July 18, 2025

      Gobe ne ranar FC Barcelona a Kano

      July 17, 2025

      On-going FISU Games in Germany: NUGA commends Dikko

      July 17, 2025
    • Column

      Ogun State’s Sports Development: My exact dream for Kano’s sports

      July 28, 2025

      Battle of Wits: As Mai Samba, Musa in leadership tussle over Pillars’ soul

      July 21, 2025

      How Governor Yusuf can accelerates sports development in Kano

      July 14, 2025

      TA, players’ recruitment: Why Kano Pillars lagging behind?

      June 30, 2025

      Death of 22 Kano athletes: My condolences to Governor Abba Kabir Yusuf

      June 23, 2025
    • News & Media

      Immortalization of 22 Dead Athletes: Good, but If I were Governor Abba…

      July 7, 2025

      Black Saturday: Stakeholders respond to 22 Kano sportsmen death…recommend strategies to prevent its recurrence

      June 16, 2025

      𝙆𝙎𝙋 starts selling online part-time application forms

      June 4, 2025

      Death of DPO, one other: Thorough investigation underway… as Police urges calm, cooperation

      May 29, 2025

      Rano avoidable carnage: Call for robust Police/Community Relation Committees

      May 29, 2025
    • Analysis

      Power tussle in Pillars: Who is who between  Mai Samba, board and Musa?

      July 16, 2025

      My disappointment with Ahmed Musa’s appointment

      July 9, 2025

      On Team Kano’s low performance at  NSF

      June 3, 2025

      KTSG’s ugly dismissal of Katsina United’s management

      April 16, 2025

      Nigeria’s stadiums safety, security: A matter of urgent attention

      December 1, 2024
    • Personality Profiles

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024

      Engr. Ibrahim Usman Aikawa: New Kano Poly Governing Council’s PAB’s representative

      August 24, 2024

      Aminu Kano 40 years after…

      April 17, 2024

      Ameh Agnes: A woman farmer of repute

      April 15, 2024

      Dr. Usman Ibrahim Aikawa: New Kano Poly, Director Academic Planning

      January 2, 2024
    Sports Eye
    Home » Gasar Kofin murnar cika shekara biyun Gwamna Abba: Mai Samba yayi hamdala
    Sports News

    Gasar Kofin murnar cika shekara biyun Gwamna Abba: Mai Samba yayi hamdala

    Sani YusifBy Sani YusifJuly 28, 2025
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram
    8

    Ba wani mahaluki a jahar Kano musamman a karamar hukumar Dala da zaifi Ali Nayara Mai Samba murna jiya Lahadi a lokacin da ya tara dubunnan matasa na cikin birni da kewaye a filin wasa na Kurna Babban Layi a wajen wasan karshe na Mai Samba Unity Cup 2025.

    Ganin dandazon jamaar da suka taro a wajen wasanne yasa Mai Samba cikin farin ciki, da annashuwa  wanda kuma ya sashi kasa zaune da kuma tsaye sai dai zirga zirga.

    Hakika taro yayi taro domin Ali Nayara Mai Samba yayi kira kuma matasa sun amsa don ta ko’ina tuttudowa sukeyi duk da haduwar hadari, al’amarin da ya tsunduma Mai Samba cikin murna da faraa tun kafin a fara wasan har zuwa kammala shi.

    Kasar wadda kungiyoyin kwallon kafa na ungowowi 28 suka shiga an shirya tane don ta ya maigirma gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru biyu akan karagar mulkin Kano da kuma ayyukan raya jiha da yake ta aiwatarwa.

    Kungiyoyin unguwa ishirin da takwas din da suka fafata a kasar sun hada da Kurna. A,

    Hotoro, Gwale, Gwammaja, Kawo, Kwankwaso, Tsakuwa , Kurna. C, Kofar Ruwa , Kofar Mata, K/Wai-Dwn, Bichi da kuma Miltara.

    Sauran sun hada da Sabon Gari, Fagge, K/Nasarawa, Dorayi, Rijiyar Lemo. B, Alfindiki, Dala, Yakasai, Brighet, Gwammaja.B, Rijiyar Lemo. A, Bachirawa, Kurna. B, Goron Dutse da kuma Bakin Kasuwa.

    A wasan karshen dai kungiyar unguwar Kurna C ce ta lallasa kungiyar unguwar Brighet da ci biyu da daya. A wasan neman na uku kuma kungiyar unguwar Mil Tara ce ta doke kungiyar  Kurna. A da ci daya mai ban haushi.

    A karshen wasan a bada lambobin yabo wanda aka fara bawa Mai Girma Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf

    Wanda an mikawa wakilin Gwamnan lambar yabonne don ayyuka tukuru da kuma kokarinsa na wanzan da zaman lafiya da kuma hana shaye shaye da kwacen waya da kuma ciyarda wasannin gaba a jihar Kano.

    Mutum na biyu da aka karrama da lambar yabo shine Hon. Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano. Wanda aka karramashi don kokarinsa na bunkasa matasa da kuma wasanni a ko’ina cikin yankin jihar nan.

    Ogan boye, shugaban karamar hukumar Nasarawa ma an karramashi saboda zama shugaba na gari don nasarorin da yake samu a mulkinsa da kuma ci gaban matasan Kwankwasiyya.

    Suraj Imam, shugaban karamar hukumar Dala ma an karramashi da lambar iya kyakkyawan shugabanci da kuma kokarinsa na cigabn jamaar karamar hukumar Dala.

    Haka kuma an karrama Sani Danja don kokarinsa na cigaban matasa a jihar Kano.

    Sabon Janaral Manaja na kungiyar Kano Pillars ma watau Ahmed Musa (M.O.N) an karramashi da lambar kokari wajen cigaban al’umma musamman a bangaren wasanni da kuma tallafawa gajiyayyu.

    Dan wasa Rabiu Ali Fagge ma an karramashi don zama fitatcen dan wasa a gasar Nayara Sallah Competition da kuma kokarinsa a wasan premier ta kasa.

    Haka kuma  Shehu Abdullahi ma ya karbi lambar yabo wajen kokarinsa na koyawa matasa wasa da kuma yin aiki tukuru.

    An kuma raba kyaututtuka ga yan wasan da sukayi shura a garsar wanda Auwal Ali Malan dan wasan Kurna A wanda yafi kowa jefa kwallaye a raga ya lashe da cin kwallo shida.

    Naziru Auwalu dan wasan kungiyar  Kurna C da Ladan Muhd na kungiyar Tsakuwa sune suka lashe kyautar kwararrun yan wasan gasar watau Best young players of the tournament.

    Haka kuma dan wasa Muhd Ahmad na kungiyar Miltara ne mai tsaron gidan da yayi fice a gasar watau Best Goalkeeper.

    Fahad Usman na kungiyar Brighet ne ya lashe kyautar dan wasan da yafi tausayi watau Fair play player of the tournament.

    Sani Zidan na kungiyar Miltara shine ya zama kocin da yafi fice watau Best Coach of the tournament.

    Kungiyar Brighet it ace ta zama kungiyar da tafi kowacce watau Best Team. Su kuma kungiyar Hotoro sune suka zama wadanda sukafi kowa da’a watau Most discipline Team.

    Da yake magana da wannan kafa, Ali Nayara Mai Samba wanda kuma shine shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ya bayyana godiyarsa ga dimbin jamaar da suka halarci wajen waccan gasar da kuma musu fatan alheri.

    Ya kuma sheda mana cewa ya yanke shawarar shirya gasarne don ta ya mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru biyu akan garagar mulkin jihar Kano.

    Mai Samba ya kuma godewa mai girma gwamna saboda irin ayyukan alheri da yake ta aiwatarwa a fadin yakin jihar Kano.

    Ya kuma yi adduar kara samun nasarori akan wadanda ake samu.

    cin kofin Gasar ta ya gwamba Abba
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleOgun State’s Sports Development: My exact dream for Kano’s sports
    Sani Yusif
    • Website

    I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.

    Related Posts

    New coach for Pillars this week? Mai Samba confirms

    July 23, 2025

    FISU Games: Prof Yakasai showers admiration on Dikko

    July 18, 2025

    Gobe ne ranar FC Barcelona a Kano

    July 17, 2025

    On-going FISU Games in Germany: NUGA commends Dikko

    July 17, 2025

    Association of Retired Sports Men and Women debut in Kano

    July 16, 2025

    Honouring 22 Kano athletes: Governor Abba Kabir Yusuf genuinely people’s governor

    June 30, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    Gasar Kofin murnar cika shekara biyun Gwamna Abba: Mai Samba yayi hamdala

    July 28, 2025

    Ogun State’s Sports Development: My exact dream for Kano’s sports

    July 28, 2025

    New coach for Pillars this week? Mai Samba confirms

    July 23, 2025

    Battle of Wits: As Mai Samba, Musa in leadership tussle over Pillars’ soul

    July 21, 2025

    FISU Games: Prof Yakasai showers admiration on Dikko

    July 18, 2025
    © 2025 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.