Daga Jamilu Uba Adamu

Tambaya : Ranka ya daɗe barkammu da warhaka, ranka ya daɗe za mu so mu ɗan ji ƙaramin tarihinka misali abinda ya shafi ma harkar wasannin golf da ya aka yi aka fara? Mai sauraro zai so ya ji wannan.

Ambassador : To jama’a Assalamu alaikum am…. wasan golf dai na fara shi ina jin yau shekara wajen goma sha biyu ko sha uku. Dalilin da ya sa kuma na fara golf, da ƙwallo nake yi har bayan na girma. akwai inda muke buga ƙwallo a nan Turona da kuma bayan Saudi Embassy, muna zuwa kowanne juma’a da Asabar da Lahadi muna buga ƙwallon ƙafa, sai na zo na ji ciwo da filin sukuwa da na ji ciwo, daga ƙwallon ƙafa sai na bar ƙwallon ƙafa sai na koma squash. ina squash shi ma na zo na yi hatsari a gurin squash na faɗi sai na bar squash. Sai na ce to tunda girma ya zo ya kamata na koma wasan da…. da wahala dai in ba tsautsayi ba a ji ciwo sai na je na fara golf. So ka ji dalilin fara golf ɗina, na yi wajen shekara 13 kenan.

Tambaya : Masha’allah ranka ya daɗe. To yanzu ga shi a gasar golf ɗin nan a cikin wannan golf ɗin da kake bugawa ga shi kuma har Allah Ubangiji ya sa ka zama shugaba ko Captain na Kano club, me za ka faɗa game wannan matsayi da Allah ya ba ka?

Ambassador : To shugabanci ka san shi na Allah ne. Ka san Allah shi yake zaɓar shugabanni. Kuma a duk inda aka haɗu aka yi tarayya, ya kamata a samu shugabanci domin a samu tsari. A, shigata na farko na shugabancin Kano Club na fara da PRO, yau ina jin ya kai shekara 10 da na yi PRO. Bayan na yi PRO yau shekara huɗu baya da suka wuce aka zaɓe ni a Captain. To ina Captain sai aka naɗa ni ambassador sai na bar ƙasa. To kuma yanzu da na gama aikina na dawo, har yanzu sai na zo na tadda an sake yin zaɓe, an zaɓe ni captain. Wannan girma ne na Ubangiji sai dai mu yi masa godiya kuma mu roƙe shi a kan ya yi mana jagora yanda za mu yi wannan abin a cikin tsari da kuma adalci.

Tambaya : Masha’allah ga gasa wacce za a fara in Allah ya kai mu ranar Juma’a zuwa ranar Lahadi. Me wannan gasa, me za ka faɗa game da wannan gasa da za a gabatar da ita a nan Kano?

Ambassador : To wannan gasa gagarumar gasa ce, dama al’ada ce shi filin golf duk lokacin da aka yi zaɓen sabon shugaba wato captain, dole ne yakan yi wasa na buɗe share fagen mulkinsa. So a wannan lokacin shi ne ake kira captain’s day. To tunda ina da abokanan hulɗa da abokanan wasa a dukka ƙasar nan da ma duniya bakiɗaya. Wannan wasa akwai mutane da yawa don a yanzu haka muna da wajen sama da mutum 200 da suka yi rajista daga nan kuma muna ga daga nan zuwa Asabar da wanda za su yi rajista a fili za mu samu ‘yan wasa sun kai 250, muna da ‘yan wasa na Kano da muka saba wasa da su, muna da ‘yan wasan Kaduna, Abuja, Katsina, Bauchi, muna da ‘yan Legas da yawa da za su zo. Har da ma abokanan wasana daga Korea, akwai waɗanda za su zo. Akwai kuma abokan wasana daga America su ma da za su zo. So, gagarumin taro ne za mu yi, za a yi kwana biyu ana wannan wasa, kuma mun gayyaci shuwagabannin da dama, da ministan wasa da ministan ƙasashen waje, da minstan al’adu na gargajiya da kuma gwamnoninmu na Kano, Jigawa da Katsina, duka mun gayyace su. Kuma wasu daga cikinsu gwamnoni guda biyu sun ba da answer cewa za su zo kuma ministoci guda biyu sun ba da answer suna zuwa.

Tambaya: Masha’allah, Captain Ali Magashi, wane fata za ka yi wa masu harkokin wasannin sanda na golf a ƙarshe ?

Ambassador : To shi wasan golf wasa ne wanda za ka iya fara shi kana shekara huɗu na haihuwa, kuma za ka iya fara shi kana shekara tamanin. So wasa ne wanda shi ya fi komai sauki, kuma wasa ne wanda zai motsa maka jiki duka jikinka gabakiɗaya, kuma ya motsa maka ƙwaƙwalwarka. To saboda haka, wasa ne da nake kiran mutanen Kano gabakiɗaya da kewaye a zo a shiga cikin wannan wasa. Kuma a yanzu yadda wasanni suka zama, sun zama hanyar samun kuɗi ga matasa. Ina kiran matasanmu su zo su shiga wannan wasa tunda yau babu ɗan wasanni a duniya da ake biya kamar ‘yan golf, saboda a yau kana jin sunan Tiger Boot, yana da sama da Dala biliyan ɗaya ta Amurka, kuma dukka a harkar golf ɗin nan ya same ta. So ka ga idan muka tabbatar yaranmu sun shiga wannan harka, to zai bunƙasa tattalin arziƙi namu kuma zai kawo lafiya a zamanmu. Kuma shi wannan fili namu mai tarihi da yawa shi ne fili na farko a ƙasar Afrika ta yamma tun zuwan Turawa ba ma Nigeria ba, tun zuwan Turawa Kano 1903 da suka zo suka ɗauki wannan fili abinda suke kira Kano protectorate suka zagaye tun daga kan Central Hotel in ka zaga ka tafi har ka je gidan Ɗan Hausa ka zagayo gidan gwamna ka tafi ka haɗa da Giginyu da Badawa ka je har Tudun Wada ka gangaro ka zagayo zuwa gidan Gwamna Shekarau har ka taho zuwa inda Nepa take Miller Road take ka shigo ka zo kan Kano Club duk su Daula su Welcare duka suna cikin wannan abu. To a girman garin Kano da ya zo an fitar da tituna an yi menene da yawa filin ya ragu sai abin da ya yi saura. To muna son mu nuna wa duniya cewa wannan fili ne na tarihi da yawa. Kuma muna son gwamnatin tarayya ta ɗauki wannan fili ta maida shi abinda ake kira nationl heritage, yadda duk duniya idan aka zo mutane za su so su san fili na farko a Nigeria za zo su yi wasa duk a kansa. To wannan zai ƙara abinda ake kira ƙarfin “tourism” a Kano. zai sa mutane da yawa su rinƙa zuwa kano saboda tarihin wannan fili idan aka gyara shi ya zo ya zama standard. To babban abin da ya sa muka haɗa wannan gagarumin taron shi ne, mu buɗe wa mutane ido a sanar da duniya cewa shi ainahin wasan nan ma a Nigeria a Kano aka fara shi, kuma mutanen Kano su san muhimmancinsa, mutanen Nigeria su san muhimmancin Kano a kan wannan harka. Kuma a sa mai ido yadda za a ci gaba da tattalin shi wannan fili ba tare da ko wata gwamnati ba ta zo da niyyar ta ce za ta karɓe fili. Saboda a yanzu wannan fili ne na wasanni ka ga bai kamata ba a ce kowanne shekara sai an caji crown trend da tournament trade da land use charges da yawa da ake yi. Ya kamata a ce gwamnati ta taimaka, to idan gwamnatin tarayya ta dauke shi, ka ga duka wannan nauyi zai ɗauke kuma za a samu hanyar da za a gyara shi.

Ambasada mun gode ƙwarai

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.