A ganawarsa da wakilin gidan Radio Nasara bayan kammala wasan kungiyar Kano Pillars da bakuwarta daga Gombe United, sabon kwamishinan matasa da wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso yayi alkawarin kawar da dukkannin matsalolin da kungiyar Kano Pillars ke fuskanta.
A cewarsa zaiyi dukkannin kokarinda yakamata yayi don tabbatarda da cewa daukacin kungiyar Kano Pillars tare da yan wasansu sun sami yanayi don yin wasanninsu cikin tsanaki da kwanciyar hankali don samun nasara mai dorewa.
Kwamishina Kwankwaso ya kuma yi alkawarin biyan duk wani bashi da yan wasan Kano Pillars kebi da kuma tabbatar da cewa ba a kuma sasu bin bashin hakkokinsu nan gaba ba.
Gameda rikicin dake tsakanin mahukuntan kungiyar kuwa, kwamishina Kwankwaso ya nuna rashin masaniyar hakan, amma yace idan har akwai hakan to dole a daina hakan.
A karshe kwamishina Kwankwaso yayi kira ga daukacin magoyabayan kungiyan Kano Pillars dasu hada kansu kuma su goyawa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf baya don cigaban gwamnati da kungiyar baki daya.