A yanzu dai ta fito fili cewa akwai tirka tirkar shugabanci babba a kungiyar kwallon kafa ta Barau wadda ita ce ta kawo sauye sayen shugabanci da aka gudanar a kungiyar a makon da ya gabata.
Wanda a makon bayanne aka bayyana nadin tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars kuma tsohon mai bawa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje shawara kan harkokin wasanni, Alhaji Kabiru Baita a matsayin mataimakin shugaban kungiyar ta Barau watan (Vice President).
Haka kuma an bayyana nadin tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Lobi, Dominic Iofa a matsayin manajan gudanarwar kungiyar.
Tun bayyana wadannan sababbin canje-canjen aka ta jin cece kuce da maganganu tsakanin magoya baya da kuma wasu daga cikin tsofaffin shuganbannin kungiyar ta Barau.
Wasu na ganin cewa yin canje-canjen a wannen lokacin kamar cin fuska ne ko kuma nuna gazawar tsofaffin shugabannin kungiyarne karkashin Ibrahim Canji duk da kokarinsu na baya.
Amma wasu na ganin daidai da maanar yin canjin domin gazawar shugabancin Ibrahim Canji da mukarrabansa ya fito fili tun fara wasan gasar firimiya ta kasa.
Samun maki biyu kacal daga wasanni hudu ne ya nuna ko fito da rashin fahimta ko kwarewar shugabancin Ibrahim Canji a kungiyar Barau kuma shine ya bada damar yin garambawul din shugabancin kungiyar.
Kowa yasan garanbawul bazai tabbata ba sai anyi binciken abubuwan dake faruwa a cikin kungiyar wanda ya sa ta tangal tangal a babban gasar kwallon kafa ta kasar nan.
Bincikenne ya nuna wasu irin zarge zagen son zuciya masu muni na gaftarewa yan wasan kungiyar albashinsu mai yawa a kowane wata.
To ni a ganina ba bawanda zaa zarga a wannan mumunan katobara irin shi mai kungiyar watau Sanata Barau Jibrin.
Saboda yadda ya dauki harkar kungiyar ya dankawa mutum daya wato Ibrahin Canji shi kadai, abinda yasashi cin karensa ba babbaka.
Koda yake naji Muktari Zico a wata fira da gidan Radiyo Nasara yana cewa yana daya daga cikin yan majalisar gudanarwar kungiyar, amma hakan bai hana abinda ake zargi ba.
Kowa yasan cewa idan kungiya nada kwamitin gudanarwa mai karfi to sune wuka sune nama wajen tafiyar da kungiyar ba mutum daya ba.
Kuma zai hana mutum daya daga cikin wadannan mutanen yin yadda yake so domin sai dukannin yan kwamiti sun amince zaa tafiyar da komai.
Amma baiwa mutum daya dama shi kadai ba karamin kuskure bane musamman idan aka duba irin yawan kudin da shi Sanata Barau yake turawa cikin kungiyar.
Amma tunda an farga an bayyana sababbin canje-canje, yakamata asa ido kuma abar kowa yayi aikin da ya kamaceshi ba tare da masa shishshigi ba. Amma fa wannan bazai hana bincike da sa ido ba don tabbatar da kowa yanayin aikinsa daidai bason zuciya.
Wani kuskure ko kuma abinda aka manta shine wasan kwallon kafa a Nijerya ba a fili kawai akeyin saba. Akwai wasu abubuwa da akeyi a bayan fage wanda mutumin da bai saniba bazai saniba.
Ina ganin rashin sanin irin wannan kinayar ne nasu Ibrahim Canji da mukarrabensa ya jefa kungiyar Barau cikin hahin da take ciki a yau.
Amma mutane da dama sunyi farin cikin wannan farkawa da Mai gima Sanat yayi saidai kuma sunyi mamakin ganin sunan irinsu tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Hon.Kabiru Baita da Dominic Iofa a cikin sabon tsarin kungiyar.
Mamakin da mutane sukeyi shine me yasa duk fadi da girman jihar Kano baaga kowaba sai Kabiru Baita da Dominic?
Wani abin haushi shi Dominic Iofa, mutum ne da ake zargi da ruguza kungiyar kwallon kafa ta Lobi dake garinsu dake Makurdi.
Da Baita da Dominic a jamaa da dama na ganin lokacinsu ya wuce domin basu da wani tarihi da suka bari a baya wanda zaisa ayi musu kallon masu nasara balantana a zaci nasara a garesu.
Wallahi tallahi a cikin garinnan namu na Kano akwai zakwakurin mutane masu hazaka da basirar da zasuyi abinda Baita da Dominic bazasu iyaba idan an basu dama.
Mutane da dama na ganin idan da gaske shi mai girma Sanata Barau yake, kamata yayi ya duba sosai ko kuma yasa ayi masa binciken na mzakwakuran mutane do zakulo masu ilmi da sannin harkar don basu damar tafi da kungiyar ba Baita da Dominic ba.
Munga gazawarsu a baya lokacin shugancinsu a kungiyoyinsu na baya na Kano Pillars da Lobi Stars don haka jammaa da dama sun zaci wasu daban.
Amma tunda an riga malam zuwa masallaci, yakamata su su Baita da Dominic suji tsoron Allah wajen yin duk abinda zaayi domin kungiyar Barau ta cigaba.
Su sani wannan kungiyar bata gwamnati bace don haka kada susa son zuciya irin wanda sukayi a baya wajen tafiyan da kungiyoyin Kano Pillars da Lobi a baya.
Su taimakawa kungiyar wajen samun madogara don samun kudin shiga masu yawa don rage bani bani wajen Sanita Barau.
Su tabbatar duk dan wasan da kungiyar zata dauka bana aro bane don idan ya tashi tafiya gaba, kungiyar Barau ta sami kudin shiga ba shiiga cikin aljihunsu dana dillalin yan wasa ba.
Su kafa Kwamitin Kwararru (Technical Committee) don taimakawa maihorarrwa samo yan wasan da kungiyar take cewa bata dasu da kuma tafiyar da kungiyar.
Kamar yadda na fada a baya cikin wani rubutu na, su duba makwabta Ghana, Niger, Kamaru da sauransu don samun yan wasan da zasu taimakawa kungiyar farfadowa.
A karshe, su sani cewa ciyarda kungiyar kwallon kafa ta Barau gaba shine ciyarda jihar Kano gaba.
Ina musu fatan alheri