A lokacin da kasa Nijeriya da jahohi ke ta kai komo izuwa kasashen waje don samo masu zuba jari a kasa da jahohi baki daya sai gashi a Kano ana kokarin hana kungiyar wasan kwallon kafa ta Barau, kungiyar da bata gwamnati ba yin wasanta na Firimiya a filin wasa na Sani Abacha, Kano.
Bayan kowa ya sani saboda gazawar kasa Nijeria tare da jahohi wajen samarwa mutanensu aikinyine yasa suke nikan gari zuwa kasashen waje don neman masu zuba jarine don samarwa yan kasa a matakin kasa ko kuma yan jahohi a matakin jahohi aki da abinyi ko kuma bunkasa kasuwancinsu.
Irin wannan tunaninne wasu daga cikin mutanenmu keyi don samawa matasa maza da mata abinyi wajen bude wasu masana’antu don taimakawa wajen dakile zaman banza a jihohi baki daya.
Ina tunanin irin wannan tunanin satata Barau yayi wajen kafa kungiyar was an kwallon kafa a jihar kano mai suna Barau Football Club, Kano.
Kungiyar wadda ta fara a matsayin Barau Academy watau makarantar koyarda wassanni ta rikide ta koma kungiyar kwallon kafa ta kuma suka sami rijistar wasan kasa na NLO daganan suka sami cigaba zuwa NNL sai kuma yanzu suka sake samun cigaba izuwa NPFL duk a cikin dan kankanin lokaci.
Mutane da yawa sun dauki wannan cigaba ne kuma abin alfahari ga duk wani dan jihar Kano kuma mai kishin Kano domin anyi abin ba sabonba.
Saidai kuma kash rashin iya siyasa yasa mutanen jihar Kano yiyuwar yin asarar wannan dama da tagomashi da Allah (SWT) yayiwa jihar Kano.
Duk da a tarihin jihar Kano baa taba samun kungiyoyin wasannin kwallon kafa na rukuni na daya ko Firimiya guda biyu a lokaci dayaba a jihar Kano ba, na dauka gwamnati tare da mutanen jihar Kano baki dayansu za suyi maraba da murna da wannan yanayi.
Saidai kash dambarwar dake faruwa tsakanin hukumar wasanni ta jihar Kano watau (Sports Commission) da shugabancin kungiyar kwallon Kafa ta Barau akan biyan miliyoyin Nairori kafin sahalewa kungiyar yin wasanta na Firimiya a filin wasa na jihar Kano abin takaicine.
Kuma wallahi idan aka bari wannan Magana ta fito fili to makwabtanmu da kuma sauran jahohi zasuyi mana dariya kuma su raina tunaninmu.
Duk da cewa yau yan kwanaki kadan suka rage sabuwar kakar wasa to kasa ta fara aiki, haryanzu an kasa samun mafita domin wata takarda da hukumar wasanni ta jiha ta nuna cewa sai kunkiyar Barau ta biya miliyan hamsin (N50million) kafin a sahale mata yin was anta na Firimiya a filin wasa na Sani Abacha.
Wannan al’amari ya daurewa jamaa da dama kai domin an dauka ita hukumar wasanni kamar yadda kowane dan jihar Kano ke ta ya kungiyar Barau murnar shiga gasar Firimiya itama murna zatayi ba yiwa kungiyar zagon kasa ba.
Wannan shi yasa jamaa da dama ke kira ga gwamnan jihar kano, Alhaji Abba Kabiirr Yusuf da ya tsawatawa ita hukumar wasanni ta jiha tare da ma’aikatar wasanni ta jihar Kano don su sake matsaya domin miliyoyin da sukeso kungiyar kwallon kafa ta Barau ta biya sunyi yawa kuma ba daidai bane.
Bincike ya nuna cewa ko kungiyar Barau ba ta yan Kano bace kuma baa Kano take ba bai kamata a dora mata harajin biyan irin wannan makudan kudin masu yawaba, balantana Kungiyar Barau kamar ta Kano Pillars da saurran kungiyoyi duk na jihar Kano ne.
Kamata yayi ita hukumar wasanni da ma’aikatar wasanni su duba taimako da gudummawar da kungiyar Barau tayi tun kafawarta har izuwa yau wajen samarwa matasan jihar Kano aiki da abinyi ba dora musu harajin miliyan hamsin ba.
Mutane da dama sun kasa gane hikimar dorawa kunkiyar kwallon kafa ta Barau wannan harraji na miliyan hamsin domin rashin dacewarsa.
Kamata yayi ita hukumar wasanni da hadin kan ma’aikatar wasanni suyi farin cikin samuwar wannann kungiya da kuma nemo mata tallafi wajen gwamnati don ragewa mai kungiyar radadin tafiyar da kungiyar ba dora musu harajin Naira miliyan hamsin ba.
Ina kira ga gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da tsawatawa hukumar wasanni da kuma ma’aikatar wasanni donyin abinda yakamata.
Bai dace mununa rashin kwarewarmu a fili ba kawai saboda bambamcin siyasa ba. Dukkaninmu yan Kano ne kuma son cigaban Kano mukeyi.
Idan kunne ya ji…