Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      Korar Yaro Yaro a Pillars: Menene laifin sa?

      November 3, 2025

      Dr. Maizare emerges VP, Karate Federation

      October 26, 2025

      Dala Hard Courts Director elected VP, Nigeria Tennis Federation

      October 26, 2025

      Dala Hard Courts Director elected VP Nigeria Tennis Federation

      October 26, 2025

      Celebrations as SWAN honours Ado Salisu

      October 20, 2025
    • Column

      NPFL: Can Kano Pillars stand test of time?

      November 3, 2025

      TSY: Accomplished talent scout, content producer, football agent

      October 27, 2025

      NPFL’s unjust and unfair treatment for Kano Pillars

      October 20, 2025

      On Shehu Adamu’s assessment of Kano Pillars’ poor performance

      October 13, 2025

      SWAN: Genuine sports stakeholder than NFF, other federation members

      October 6, 2025
    • News & Media

      Happy birthday, Magistrate (Coach) Ibrahim Gwadabe

      November 3, 2025

      Kidney Patients send SOS to Governor AKY

      October 29, 2025

      Ganduje named Mi-Yetti Allah’s adviser for youth empowerment

      October 25, 2025

      Few minutes in the midst of lawyers

      October 24, 2025

      Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

      October 22, 2025
    • Analysis

      Matsalar Kano Pillars ibtala’ice, amma…

      October 28, 2025

      Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

      October 22, 2025

      Technical Advisor, Assistant for Kano Pillars Suspended: What’s next for Sai Masu Gida?

      October 21, 2025

      Korar Ogenye da Yaro Yaro: Ba su suka kar zomon ba

      October 20, 2025

      Rashin kokarin Kano Pillars da Barau: Sai fa gwamnati ta yi wani abu

      October 7, 2025
    • Personality Profiles

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024

      Engr. Ibrahim Usman Aikawa: New Kano Poly Governing Council’s PAB’s representative

      August 24, 2024

      Aminu Kano 40 years after…

      April 17, 2024

      Ameh Agnes: A woman farmer of repute

      April 15, 2024

      Dr. Usman Ibrahim Aikawa: New Kano Poly, Director Academic Planning

      January 2, 2024
    Sports Eye
    Home » Kwanaki darin Hajiya Hauwa Isa Ibrahim na jagorancin ARTV
    News & Media

    Kwanaki darin Hajiya Hauwa Isa Ibrahim na jagorancin ARTV

    Sani YusifBy Sani YusifSeptember 10, 2024
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram

    A makon da ya gabatane watau ranar 6 ga watan Satumbar wannanshekarar ta 2024 , mai rikon mikamin shugabancin Gidan Talabijin na Abubakar Rimi(ARTV), Hajiya Hauwa Isa Ibrahim ta cika kwana dari cif da darewa kan mulkin gidan talabijin din.

    Zamanta mai rikon mikamin shugabancin gidan watau (Acting Managing Director)  Abubakar Rimi Television (ARTV) ke wuya, Hajiya Hauwa ta farfado da gidan daga dogon suman da yayi saboda rashin kulawa da kuma sassaita ayyukan gidan talabijin din ta hanyar bada  shugabanci nagari wanda ya sami rauni daga shugabannin da suka shude.

    Babu shakka kwana darin da Hajiya Hauwa tayi tana jagorancin ARTV, kwanaki ne masu tarin albarka saboda darurruwan cigaban da ta kawu gidan talabijin din wanda a lokutan baya ake kira CTV 67.

    Kasancewarta shugabar ARTV keda wuya, Hajiya Hauwa ta fara saitawa maaikatan gidan alkibla don su rinka zuwa aiki da kuma tashi akan lokaci.

    Nan take ta dakatarda zuwa aiki a makare da kuma fashin zuwa aiki wanda a lokutan baya yasha kan gidan.

    Tunda masu iya magana suna cewa, daga na gaba ake  ganin zurfin ruwa, Hajia Hauwa ta fara nuna kyakkyawan misali wanda yasa ita ke fara zuwa aiki kullum don nunawa sauran maaikatta abinda ya kamacesu.

    Jagoriyar ta  gyara dangantakar shugabancin gidan da dukkannin ma’aikata wanda shine musabbabin samun dinbin nasarorin da ta samu a wadannan kwanaki dari masu tarin albarka. Saboda kowane maaikaci a halin yanzu na aiki tukuru da kuma kula da kuma bin nagabansa.

    Sanin mahimmancin ma’aikatane yasa  Hajiya Hauwa daukar hakkokinsu da muhimmancin gaske wanda yasa ta sasu a gaba da kuma gabatar dasu a duk lokacin da aka kawo mata gabanta.

    Haka kuma shugabancinta ya samawa gidan sababbin  kayayyakin aiki na zamani a kusan kowane bangare da suke bukatarsu don inganta ayyukan ma’aikatan.

    Hakan yasa daukacin maaikatan gidan talabijin din ARTV tashi tsaye da kuma daukar aikinsu da mahimmanci ba dare ba rana wanda ya kyautata sauti da kuma hotunan da talabijindin take yadawa.

    Wani abu daya da Hajiya Hauwa Isa Ibrahim shine, macece mai haba-haba da kowa da kowa  amma bai hanata tsawatawa ba domin batason wasa da aiki.

    Saboda tabbatar da cewa ayyuka na tafiya daidai,  Hajiya Hauwa ta aiwatar da gyare-gyare a dakunan dakunan  yada labarai na gidan (Studio) da kuma samarda na’urorin daukar hotona da kuma komputoci na kan tebur (Desktop) da na kuma kan cinya (Laptop) duk don samun saukin aikin maaikatan gidan.

    Hajiyar ta kuma samarda manya-manyan abubuwan saukewa da kuma ajeye labarai, hotuna da kuma fina-finai don amfani dasu nan take ko kuma nan gaba.

    Ta samarda sabuwar na’urar wuta (transformer) da kuma gyara injin bada wuta na wucin gadi don samun wutar lantarki akowane lokaci.

    Bakamar da ba, Hajiya Hauwa tayi nasarar mayar da shirye-shiryen gidan talabijin din ARTV awa ishirin da hudu ba dare ba rana, al’amarin da yasa gidan  samun karin masu kallo a fadin duniya bakai daya. Abinda yasa Hajiya Hauwa zama shugabar gidan ta farko da ta ciri tuta da samun yabo ta ko’ina a fadin yakin jiharnan da kuma duniya baki daya.

    Hajiyar wadda mafi yawan mutane ke mata kirarin “Mace mai kamar maza” saboda kokarinta da kuma aikitukurunta ta kuma sami nasarar dora shirye-shiryen gidan ARTV din kan Tauraruwar NIGCOM SAT abinda yasa ganin shirye-shiryen gidan ARTV din a dukkannin fadin duniya.

    Hajiya Hauwa ta kuma zamanantar da shirye-shiryen gidan talabijin na ARTV ta kuma yada ayyukansa kan kafofin sadarwa na Twitter, Instagram, Facebook, da kuma TikTok, al’amarin daya karawa gidan masu kallo, saurare da kuma karanttawa a fadin duniya baki daya.

    A halin yanzu Hajiya Hauwa ta kuma maida ARTV kafa ta farko wajen nunawa da kuma tallata dariruwan ayyakan alheri da mai girma Gwamnan jihar Kano, Injiya Abba Kabir yaketa aikatawa a fadin jihar Kano.

    Wannanne yasa a lokacin da mai girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido kwanan baya, gwamannya yaba mata sosai saboda ganin ayyukan da ta aiwatar da kudaden   da ya sahale mata don gyara gida ARTV din.

    A dukkannin bangarorin daya ziyarta, gwamna sai murmushi yake tayi saboda gamsuwa da abubuwan da yaganewa idanunsa.

    Don haka jamaa da dama ke adduar cigaba, nasara da kuma daukaka ga Hajiya Hauwa a dukkannin ayyukanta da kuma inda ta sami kanta yanzu da kuma nan gaba.

    Haka kuma, soyayya da kuma kaunar gwamna yasa ta daukar nauyin gabatar da bikin wasan gasar kwallon kafa ta kananan hukumomi 44 na jihar Kano saboda murnar cikarsa shekara daya a bisa mukin Kano.

    A karshe dole a godewa mai girma gwamna wajen zakulo ita Hajiya Hauwa Isa Ibrahim da kuma dora ta kan wannan mukamin. Ga kuma bata hadinkai a inda yake amincewa da dukkannin abubuwa da ta kawo gabansa.

    Fatanmu shine mai girma gwamna ya tabbatar mata da mikaminnata don samun natsuwar da cigaba da inganta ayyukan ARTV da kuma tallata da kuma yada ayyukan mai girma gwamna.

    ARTV jagorancin Kwanaki dari
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleKano Pillars Media directorate: Good initiative, but…
    Next Article Celebrating 100 Days of sports loving Acting ARTV MD, Hajiya Hauwa Isa Ibrahim
    Sani Yusif
    • Website

    I was a staff of the then Triumph Newspapers, with keen interest in sports journalism which drove me to the unit where I was supported and oiled in the dynamics of modern sports reporting by my mentor/friend, Sani Zaria, the then Group Sports Editor of the Triumph. And when he left in 1995, I tried to sustain the spirit against all odds with a column sportesye. But when The Triumph was closed, I was moved to Kano Polytechnic as a lecturer until my retirement last 3 years, which gives me time to return to what I know best , the recreation of the SPORTS EYE.

    Related Posts

    Happy birthday, Magistrate (Coach) Ibrahim Gwadabe

    November 3, 2025

    Kidney Patients send SOS to Governor AKY

    October 29, 2025

    Ganduje named Mi-Yetti Allah’s adviser for youth empowerment

    October 25, 2025

    Few minutes in the midst of lawyers

    October 24, 2025

    Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

    October 22, 2025

    Re-Extortion at Urology Center: Gov Abba must hear this

    October 10, 2025
    View 1 Comment

    1 Comment

    1. Zahraddeen zakari on September 10, 2024 2:54 pm

      Masha Allah

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    Happy birthday, Magistrate (Coach) Ibrahim Gwadabe

    November 3, 2025

    Korar Yaro Yaro a Pillars: Menene laifin sa?

    November 3, 2025

    NPFL: Can Kano Pillars stand test of time?

    November 3, 2025

    Kidney Patients send SOS to Governor AKY

    October 29, 2025

    Matsalar Kano Pillars ibtala’ice, amma…

    October 28, 2025
    © 2025 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.