Hakika anga cikar dakin taro na gidan gwamnatin jihar Kano (wanda ake kira Corronation Hall) ya cika makil ranar wata Talatar wani mako da ya gabata.
A wancen makonne akaga wasu daga cikin gagga-gaggan jam’iyyar APC da wasu daga cikin manyan jami’en gwamnatin jihar Kano wajen halartar bikin canja shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC.
Cikin manyan bakin da suka halarci wajen taron daga bangaren APC sun hada da tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakin shugaban majalisar Dattijai, Sanata Barau Jibrin.
An hangi yan majalisar tarayya na bangaren APC da kuma wasu kadan daga bangaren Kwankwasiyya sai dai mataimakin gwamna Comrade Abdussalamu sam baaga keyarsa ba.
Anga halartar shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano watau Abdullahi Abbas da kuma sauran jiga-jigan APC na jihar Kano a wajen.
Wannan ko wadannan sune tabbacin komawar gwamna Abba jam’iyyar APC mai mulki a kasata Nijeria.
Amma wani abin tambaya da mamaki shine, ba kamar yadda aka gudanar da taron komowar gwamnonin Bayelsa, Pilato da na Taraba ba, inda mataimakin shugaban kasa, Kassim Shetima da jigogin jam’iyyar APC ta kasa sukayi tururruwa ba.
A Kano an sami akasi hakan domin ba’a ga keyar kowa daga cikin wadancen manyan mutanen da aka zayyana ba a wajen taron komawar gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC ba.
Menene wannan yake nufi? Ace gwamna guda irin na jiha kamar Kano ace babu fuskar wani jigo na jam’iyya na kasa a wajen karbarsa.
Wannan kuma ni a wajena rashin tabbacin komowarsa APC amma koma menene ake boyewa lokacine kadai zai bayyanawa mutanen jihar Kano shi ko kuma ya fito fili.
Allah yasa mu dace.
