A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne Allah ya yiwa Hajiya Juwairiyya Yusuf rasuwa.
Mai shekaru 75, marigayiyar ta rasu a asibiti bayan gajeriyar jinya. Hajia Juwairiyya ta rasu tabar ‘yaya uku da jikoki goma sha biyu.
Cikinsu yaran da ta bari akwai Maimunat, Dalhat da Saadatu. Dalhat tsohon maaikacin Maaikatar Ruwa ta Zaria ne wanda a yanzu kuma yana babban maaikacine a Hukumarar shirya jarabawar makarantun Arabiyya da Islamiyya ta kasa mai suna NBAYES.
Mamaciyar kuma kanwa ce kuma wajen Alhaji Abubakar Dogara Yusuf kuma ansanata da hukuri, uriya da son yan uwada zumunci.
Allah yaji kanta ameen.