Sabon zababben shugaban kungiyar yan kasuwar Kurna Asabe Babban Layi Alhaji Mustapha Umar Malikawa yayi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta samo wani bigire wanda zata taimakawa yan kasuwa saboda halinda yawancinsu suka fada.
Malikawa ya yayi wannan kiranne ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da aka rantsar da su a unguwar Kurna Asabe.
A cewarsa yan kasuwa da yawa sun fada cikin halin ni’yasu saboda rushewar jari wanda yanayin rashin ciniki ga kuma tsadar kayayyaki wanda matsin rayuwa ya haifar.
Saboda haka, Alhaji Malikawa yayi kira ga gwamnatin jiha da ta kawo musu dauki.
Samarwa yan kasuwa jari zai taimakawa jamaa awannan lokacin, shugaban yace.
Sabon shugaban kuma yayi alkawarin yin iya kokarinsu don inganya rayuwa da kuma kasuwancinsu a gaba dayan kasuwar tasu.
A karshe ya kuma nemi goyon bansu don cigaban kasuwar tasu.
Mutane da dama sun halarci bikin cikinsu harda Barrista Hussaini Ahmed Makari, Sarkin kasuwar Alhaji Abdulwahabu Umar Sanda da sauran jamaa.