Kora ko dakatar da masu horar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars guda biyu watau Evans Ogenye da Ahmad Garba Yaro Yaro da kwamitin gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars tayi jiya wani salone na dorawa mara laifi laifi.
Kwamitin ya sanarda dakatarwarne jim kadan da kammala wasan kungiyar ta Kano Pillars da takwararta to Barau a filin wasa na Sani Abacha inda kungiyar tayi rashin nasara da ci biyu da daya.
Saboda rashin gamsuwa da kwamitin yayi da sakammakon da kungiyar Kano Pillars ke samune yasa kwamitin gudanarwar darkatar da Ogenye da Yaro Yaro har sai illa masha Allahu.
Rashin tagazawar kungiyar ya fito filine cikin wasanni takwas da kungiyar tayi a inda ta ci biyu da yin kunnen dokin wasanni biyu sannan kuma tayi rashin nasarar wasanni guda hudu.
Kwamitin kuma ya umarci tsohon Kaftin din kungiyar kuma mataimakin mai horaswa, Gambo Muhammad tare da mai horarda masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu su cigaba da aikin horasda yan wasan har zuwa wani lokaci.
Ni aganina wannan mataki da kwamitin gudanarwar ya dauka bai dace ba kuma ba daidai bane musamman a wannan lokacin.
Rashin dacewar kuwa aganina ya bayyana ne saboda kinyin abinda yakamata kwamitin yayi daga lokacin kamala kakar wasa ta bara izuwa wannan kakar wasan ta bana.
Kowa idan zai iya tunawa, a lokacin da sauran kungiyoyi ke ta kokarin yin garanbawul a kungiyoyinsu ta hanyar daukar kwarraru da fitaccun yan wasa da kuma sallamar wasu, ita kungiyar Kano Pillars sharbar bacci kawai take tayi.
Haka kuma, kasa saurin samo mai horadda yan wasan kungiyar da gaggawa tun lokacin tafiyar Usman Abdallah wani abin dubawane.
Na san a baya magoya bayan kungiyar da yawa sun koka yadda kungiyar ta kasa bayyana sunayen sababbin yan wasan da suka dauka ga kuma rashin mai horaswa, amma mahukuntan kungiyar sukayi tsit.
A sanina kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillar ce kawai ta kasa bayyana sunayen sababbin yan wasan da ta dauka balantana wadanda ta sallama.
A ganina laifin kwamiti zaa gani bana masu horaswaba domin da sunyi abinda ya kamata a lokacin da yakamata da ba wannan zancen akeyi yanzu.
Yan wasane ke busa wasa ba masu horaswa ba, kuma da abinda aka basu ko suka taras dasu za suyi aiki.
Kowa yasan sai fa da suka gama daukar yan wasa sannan suka samo mai horaswa wanda ya saba da yadda aka sani.
Kowa yasan sai an dauki mai horaswa ake kuma bashi dama ya duba yan wasan da ake dasu da kuma kawo wadanda yake ganin zaa cuke gurbi da su.
Naji masu sharhin wasanni da dama suna fadar rashin kwarrarru da goggaggun yan wasa a kungiyar.
Amma fa ba’a makara ba, yakamata kwamiti yayi sauri ya duba inda ake da matsala a kungiyar sannan a nemo wadanda zasu cike gurbin matsalar koda a kasashe makwabtane.
Nasan gwamnatin mai girma Abba Kabir Yusuf a shirye take ta bawa kungiyar dukkanin hadin kai da taimakon da take nema don cigabanta.
Allah yasa mu dace, amen.