A tabbatarwa da daukacin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars cewa kungiyar na mamaye a zuciyar mai girma gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Mai rike da mukamin kwamishinan wasanni kafin nadin sabon kwamishinan wasannin, Hon. Kachako ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ayarin yan jaridar gidan Radiyon Nasara bangaren wasanni  a ofishinsa.

A cewarsa mai girma gwamna na sahale dukkan wani roko ko bukata daga shugabancin kungiyar Kano Pillars da sun iso ofishinsa ba tare da bata wani lokaci ba.

Don haka kwamishinan ya ja hanklin magoyabayan kungiyar cewa gwamnatin Kano bazata taba barin kungiyar Kano Pillars cikin wani halin rashin kudi ba wanda har zai sa ta kasa zuwa ko samiin tsaiko wajen zuwa wasanninta na waje ba.

Hon Kachako ya kara da cewa matsalolin da aka dan samu daga farko na rashir samun kudin da zasu fara gudanar da kungiyar ne wanda shi ya haifar da akasarin wadancan matsaloli.

Idan baa manta ba cewar Hon. Kachako an sami rigingimu tsakanin shugabannin gudanarwa na kungiyar wanda yasa suka tashi tsaye suka magance su baki dayansu.

Kwamishina Kachako ya kuma godewa yan wasa da masu horar dasu saboda kokarin da sukayi har kungiyar Kano Pillar ta zaman a uku kafin zuwan azumi wanda ya rage musu karsashi kuma sukayi baya kadan.

Katcako yayi kira ga yan wasan kungiyar dasu dage su koma matsayinsu tunda azumi ya wuce kuma baki ya bude.

A game da walwalar yan wasa kuwa, kwamishina Katcako ya shedawa ayarin Nasara Radiyo cewa ita ce a gabansu domin zuwansa ya karawa yan wasa kasha dari na aalawus dinsu kuma ya bada umarnin a dinga sama musu wajen kwanciya mai alfarma a duk lokacin da sukaje wasa wajen jiharnan.

“Kai nan bada dadewaba muna tunanin kara musu albashi don su sami kwanciyar hankalin buga wasa da kuma samun nasara a duk lokacin da suke wasa gida ko waje,” cewar Hon Katcako.

Kwamishin ya kuma tabbatarwa daukacin magoyabayan kungiyar Kano Pillars cewa suna duba yiwuwar kai yan wasan kungiyar wasanninsu na waje a jirgin sama don zamun hutu da buga wasa a tsanake.

Game da karin albashin yan wasa kuwa, Hon. Katcako yace nan gaba kadan zai nemi sahalewar mai girma gwamna don kara albashin yan wasa.

Game da jita jitar zuwan yan wasan Kano Pillars a kafa daga gida, kwamishina Zatcako yace bashi da labarin hakan amma zai bincika kuma idan an tabbatar zaa hukunta masu hannu a ciki.

“Muna da hotel da muke kamfin yaran mu a dukkanni lokutan wasanninmu na gida don haka ya karyata masu cewa baa kamfin saboda rashin biyan kudin hotel.

Kwamishina ya kuma karyata masu cewa matsalar Kano Pillar daga maaikatar wasannni take. Maaikatar wasanni bata da wani aiki sai taimakawa Kano Pillars ba akasin hakan ba, cewar Hon. Katcako.

Kwamishin ya kuma tabbatarwa daukacin jamaar Kano cewa akwai wani shiri na musamman da akeyi don saita kungiyar don yin fice a kakar wasanni ta badi.

Game da zaargin rashin sakarwa kungiyar kudin tafiya wasanni da wuri kuwa, kwamishina katcako ya bukaci kowa da kowa da a tsoraci Allah a daina soki burutsu.

“A sani fa kafin kungiyar ta kawo bukatar kudin tafiya jihar Edo muka sama mata dukkannin kudin da suke bukata’, cewar Katcako.

“Burinmu a kullun shine jin dadi da walwalar yan wasan Kano Pillars,” in ji Hon. Katcako.

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.