Hakika ina matukar mamakin jin maganar cewa bashi yayi wa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars katutu wasu ma na cewa kungiyar taci bashi har iya wuya.
Mamakin da na keyi yana faruwane saboda wasu tambayoyi da nake dasu wanda kuma nake bukatar amsarsu daga mahukuntan kungiyar.
Tambayoyin nawa kuwa sune, ina mahukuntan kungiyar Kano Pillars suka kai dimbin kudin da suka samu wajen sayar da tsofaffin yan wasan kungiyar kafin fara wasan kakar wasanni ta bana?
Kowa yasan cewa idan wata kungiya ta dauki yan wasan wata kungiya to ya zama dole kungiyar ta biya kudin taransifa din wannan ko wadannan yan wasan da ta dauka.
Bugu da kari ina bukatar sanin inda ko yadda kungiyar Kano Pillars ta kai miliyoyin kudin da ta samu a yar jejeniyar da suka kulla don saka tallar sunan wani kamfani a gaban rigunan yan wasansu.
Ina kuma so mahukuntan kungiyar suyi mana bayanin miliyoyin kudin da suke samu a lokacin wasannin kungiyar na gida.
Rashin sanin amsar wannan tambayar ya sani mamakin yadda mahukuntan kungiyar suke ta yayata sunnan gwamnati don rashin basu kudi.
Sai mun sami cikakken bayani akan wadannan tambayoyi kafin ni da ire-ire na mu yarda kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na bukatar kudi.