Idan mai karatu mai bibiyar kafofin sadarwa na yanar gizo ne zai iya yin kicibis ko kuma samun labarin kiran da wata hajiya a jihar Kano keyi na kira da rokon mai girma gwamnan jihar Kano injniya Abba Kabir Yusuf da ya tashi filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata daga inda yake.

Hajiyar mai suna Ain Jafaru Fagge wanda kowa yasanta a  matsayinta na sananniyar yar siyace ta bada dalilan kiran da korafin nata ga mai girma gwamna saboda abubuwan da suka biyo bayan kafa filin wasan tun lokacin da aka kafa shi har izuwa yau.

A cewar ta, kasancewar  filin wasan na Kofar Mata a wajen da yake na cutarda mutane da yawa musamman na asibitin Murtala don ana firgita marasa lafiya da akeyi duk lokacin da aka kamala wasa a filin.

Hajiyar ta kara da cewar  ana cutar kuma da mutanen Kofar Mata wajen shigar musu gida da makamai da akeyi, tare da mutanen Koki da mutanen Fagge.

Hajiyar ta kuma kara da cewa har yan kasuwar Singa, Wapa da na kwari dana Sabon Gari duk na cutuwa da illar da abinda ke faruwa a duk lokacin da akayi wasa a filin wasa na Kofar Mata.

Ta bada shawarar fidda filin wasan na Kofar Mata wajen gari domin a ganinta nanne yafi dacewa da shi.

Amma wani abu da hajiyar ta manta ko ta kasa ganewa shine, suwaye masu aikata barnar? kuma su waye suke daure musu gindin yin barnan? Ko kuma su waye iyayen gidan su?

Sufa wadannan masu aikata wannaan danyen aikin da Hajiya Ain Jafara take ta kwakwazo ba wasu bane illa yaransu ne. Kuma su suke daure musu gindin yin abinda sukeyi. Su suke sawa ana sakinsu domin yaransune.

Ya kamata Hajiya ta sani cewa kowa ya san inda ta nufa da korafinta. Ba dan Allah tayi korafin ba. In ina ganin turo ta akayi.

A ganina so kawai ake a sami kafar rushe filin wasan da aka kashe makudan kudin kasarnan wajen ginawa don ita da irinta su sami kasonsu na mallakar filayen gina shaguna.

Wani abin da Hajiya ta kara mantaewa shine, a fadin jiharnan kaf dinta ba masu taimakawa lalacewar matasanmu irinsu yan siyasa. Domin yan siyasa ke daure musu gindin yin munanen ayyukan da sukeyi.

Na duba kaf fadin jiharnan ban ga inda wani malami ko dan kasuwa ko basarake ke ajiye ko tafiya da yan daba da shaye-shaye ba.

Yan siyasane kawai ke lalatasu kuma su suke amfanarsu gashi kuma abin kunya tana  kukawa da dasu.

Duk masu irin wannan mummunar bukata don kawai sunason a mallaka musu filin gina shaguna idan an rushe filin wasan bazasu sami nasara ba. Domin miliyoyin masu ruwa da tsaki na harkar wasanni baza su barsu ba.

Cewar a wasu kasashe filayen wasa a wajen gari suke, ba daidai bane  domin idan ta duba filinye wasanni na kasashen turai duk a cikin jama suke baa gefen gari ba.

Na dauka Hajiya yanzu zatayi kira ga mai girma gwamana ya duba mummunan halin da makarantun firamaren yayan talakwwa suke.

A halin yanzu ba wata firamare da dan talaka ke zuwa wadda ke da abin zama balantana na rubutu.

Ko kuma me yasa Hajiya bazatayi kira ga mai girma gwamna da yasamawa yaran abinyi ba?

Kifi na ganinka mai jar koma.

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.