Yau wata uku cif da zuwa da dawowar yan wasan jihar Kano daga wasan kasa na nakasassu watau (2023 National Para-Games Competition) wanda akayi a Abuja amma har yanzu hukumar wasanni ta jihar Kano (Kano State Sports Commission) bata biya mafi yawancin yan tawagar zuwa Abujan hakkokinsu ba (Daily Travelling Allowances).
Wani abin haushi datakaici wanda kuma ya zubarwa da hukumar wasannin ta jihar Kano mutunci a idon jamaa shine kasa wani katabus don karbowa mafi yawancin yan tawagar hakkokinsu daga gwamnati kamar yadda suke cewa.
Bincike ya nuna mummunar wahalar da dukkannin yan tawagar jihar Kano suka sha a lokacin da suke Abuja gabadayansu saboda rashin biyansu alawus din da yakamata a basu tun kamin tafiyar tasu zuwa babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.
Idan bamu manta ba, hukumar wasan ta jihar Kano ta tura yan wasa, masu horar dasu, sakatarorin tsare-tsare, likitoci, yan jarida, direbobi, jami’en tsaro da sauransu zuwa Abuja ba tare da basu kudaden alawus dinsu ba (DTA) da alkawarin damka musu kudadensu da sun isa Abuja.
Amma wani abin takaici da suka isa Abuja sai hukumar wasannin tayi musu kememe al’amarin da ya jefa dukkannin yan tawagar cikin rudani da dimuwa saboda tsanani rashin kudi da suka shiga.
Wannan ya faru ne saboda mafi yawancinsu basu da kudin cin abinci balantana na inda zasu kwanta ga shi kuma basusan kowa a Abuja ba. Ga kuma rashin kudin sufuri daga can zuwa can.
Da wuya tayi wuya sai suka koka ta hanyar yan jaridun da suke tare dasu wanda yasa mukaddashin hukumar wassannin ta jihar Kano, Malam Bala Malam magantuwa.
A jawabinsa ga yan jarida Malam Bala ya bayyana karbar Naira miliyan tara (N9m) cikin miliyan 30 da suka nema daga gwamnati wanda kuma a cewarsa yayi amfani da kudin ya biya kudin rijistar yar wasa al’amarin ya rudarda jama’a da dama.
A wancen lokacinne Malam Bala yayi alkawarin biyan kowa alawus dinsa da zarar sun komo gida jihar Kano.
Bincike ya nuna mafiyawancin yan tawagar mutanene masu iyali kuma sun bar gida da alkawarin da sun isa Abuja zasu turowa iyalensu kudin kashewa wanda rashin biyan ya jefasu cikin wata dimuwar.
Wani abin haushi kuma shine da suka komo gida alkawarin bai cika ba domin mukaddashin shugaban hukumar yayi biris da maganar, al’amarin da yasa yan tawagar kara magantuwa ta kafafaen yada labarai masu dama.
Wannance ta firgita shi inda yaje ya samo kudi amma kash a maimakon ya biya dukkannin yan tawagar sai ya zabi wasu a cikinsu har da yan jarida ya biya ya kuma manta da sauran. Al’amarin da jama’a da dama sukayi Allah wadai da kuma kokarin toshe bakin masu magana wanda yayi nasara.
Wani karin abin takaicin kuma shine cikin mutanen da Malam Bala yaki biya akwai likitoci da dirobobi wadanda arosu akayi daga wasu ma’aikatu don su taimaka a sami nasarar tafiyar.
Bugu ga kari su kuma sauran kamarsu sakatarori su suke samo masu horarwa sannan su kuma masu horarwa su samo yan wasa.
Amma ya biya yan wasa ya manta da sakatarori da masu horarda yan wasan wanda shima babban koma bayane.
A ganina biyan wasu yan wasa da kuma kin biyan wadancen jami’en ba daidai bane kuma ya nuna rashin sanin aiki da kuma rashin iya gudanarwa.
A nan nake tunawa Malam Bala yadda ya karbo naira miliyan tara ta farko daga cikin miliyan talatin da gwamnati ta amince a kasha da kuma kudin ya kara amsowa wadanda bamusan yawansu ba ya biya wasu yan wasa da yan jarida, yakamata ya yi namijin kokari wajen nemo sauran kudaden ya biya masu hakki hakkinsu.
Yakamata Malam Bala ya sani cewa shi shugabanci ba zama ko iya zama a ofis bane. Yin abin da yakamata a lokacin da yakamata shine shugabanci.
Yin shiru ba gwaninta bane domin a watan goma sha daya za a sake wani wasan, da wane ido ko fuska zaa kara neman wadannan mutanen don samun gudummawarsu?
Bugu da kari, shugaban hukumar wassannin yakamata ya sani cewa da wadannan mutanen da bayaganin kimarsu da mutuncinsu basu agazaba, da tafiyar zuwa Abuja bata yiwu ba
Tun da har mai girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince a biya banga dalilin da Malam Bala zai rinka baya-baya ba. Ya tashi ya je inda ya kamata don karbowa mutane hakkinsu.
Ya kuma kamata Malam Bala ya fara amfani da kudaden shiga da hukumarsa take samu daga sitadia ta Sabon Gari da ta Kofar Mata da kuma filin wasa na Ado Bayero Squre don fara rage kudin kafin ya amso wadancan.