Kwanaki masu yawa da sanarda rushe hukumar gudanarwar riko ta kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wadda Babangida Little ke shugabanta har izuwa yau bata sake zani ba domin bai sauka ba kamar yadda aka umarceshi.

Duk da yake umarnin da gwamnati ta ba wa Little ta bakin kwamishinan harkokin matasa da wasanni, Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso na mika harkokin gudanar da kungiyar ga babban jami’in gwamnati a kungiyar, wannan ba ta samu ba domin har yanzu baayi ba..

Mutane da yawa sun sa ido suga rana ko lokacin dashi tsohon shugaban kungiyar Kano Pillars, Babangida Little zaibi umarnin gwamnatin jiha amma abin haushi da takaici har izuwa yau  rusasshen shugaban kungiyar Kano Pillars din yakiyin abinda gwamnati ta umarceshi yayi.

Wannan ta sa masu ruwa da tsaki kallon yanayin a matasayin  raini da rashin ladafi ga gwamnati da kuma gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Yawancin masu ruwa da tsaki sunyi maraba da murnar rushe shugabancin Little saboda tarin matsaloli da ya haifar da rashin bin ka’idar aiki a kungiyar.

Yawancin mutanen da suke ta tofa albarkacin bakinsu a wannan tata-burza  na ganin nuna rashin kima da ladabi ga gwamnati da Little yayi ta hanyar kin bin umarnin gwamnati da yayi.

Mutane da yawa suna mamakin yadda Little yayi kememe yaki mika harkokin kungiyar ga wanda aka umarceshi yayi.

Jama’a da dama sunyi mamakin yadda akaga Little da tsohon sakataren kungiyar Abbati Sabo a mota zuwa Abuja wajen taron shekarashekara na kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa watau NFF.

Haka kuma ganin mutumin das hi babangida Little ya aiyana a matsayin sabon mai hurarda yan wasan kungiyar Kano Pillars din na nan daram a Kano sa sake sa mutane shakku.

Bayan haka wasu take-taken Little yana sake sa tsoro da shakku  a zuciyoyin masu ruwa da tsaki kan cewa ko shi Little yafi karfin gwamnatine?

Sai dai jiya a wajen bude gasar wasannin masu damara na jihar Kano, anji shugaban ma’aikata na fadar gwamnati jihar Kano, Hon. Shehu Wada Sagagi na tabbatar da rushe kamitin gudanarwar Kano Pillars.

Sagagi  kuma ya sake tabbatar cewa kowane lokaci  gwamnati zata nada wadanda zasu cigaba da shugabancin kungiyar Kano Pillars.

“Kwamishinan wasanni na nan na zakylo wadanda zaa nada don shugabanci nagari ga kungiyar, cewar Sagagi.

Sai dai rashin nada wadanda zasu shugabanci kungiyar har yanzu yana sake kawo shakku saboda rashin issasshen lokacin fara shirin fuskantar sabuwar kakar wasanni mai zuwa wadda zata fara a watan gobe.

Yanzu dai zaa sa ido aga yadda zata kaya.

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.