Ana wata ga wata, domin a daidai lokacin da kungiyar kwallon kafa ta Barau ta bankado wasu almindahanonin kudi masu nauyi da ake ta tafkawa a kungiyar wanda kuma ake zargin shugabancin Ibrahim Shitu Canji yakeyi, sai gashi Ibrahim Canji na nuna wasu halaye ga kungiyar wadanda basu kamata ba ko kadan.
Wata majiya mai tushi ta shedawa wannan kafa cewa tun lokacin da aka bankado almindahanonin zabtarewa yan wasan kungiyar Barau kusan rabin albashinsu yasa mamallakin kungiyar, Sanata Barau Jibrin Maliya ya umarci da gabatar da canje-canje a tsarin shugabancin kungiyar.
Yin binciken ke da wuya aka bankado wani abu mara dadinji, watau yadda ake zabtarewa wasu daga cikin yan wasan kungiyar Barau din rabin albashinsu ba gaira ba dalilin kuma babu dalilin yin hakan.
Haka kuma rashin samun nasarar kungiyar ta Barau a wasannin da ta buga guda hudu duk da makudankudin da ake kashewa kungiyan ya bayyana rashin kwarewa da gogewar shugabancin Ibrahim Shitu Canji a harkar wanda shima ya taimaka wajen samarda canje-canjen a kungiyar Barau din.
Hakika canje-canjen wanda ya kawo wasu mutum biyu masu kwarewa da ilmin abin ya ragewa shi Ibrahim Shitu Canji karfin fada a ji a kungiyar sosai, abinda ake ganin shi ya hasala shi.
Shi wannan canje-canjen ya shigo da tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Alhaji Kabiru Baita, a matsayin maitaimakin shugaba da kuma Dominik Yofa, tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Lobi dake jihar Binuwe, a matsayin babban manajan kungiyar kwallon kafa ta Barau.
Ko shakka babu wata majiya ta tabbatarwa wannan kafa cewa wannan al’amarin baiyiwa Ibrahim Canji dadi ba domin a da shine ke da wuka kuma shine da nama domin Sanata Barau ya bar masa komai a hannunsa.
Amma kash, a maimakon shugabancin Ibrahim Canji yayi abinda yakamata, sai a wata majiya suka kawo son zuciya wanda baiyiwa shi Sanata Barau da kungiyar dadi ba wanda ya jawo samarda wani tsari da zai shigo da wasu don daidaita al’amarin.
Hakika shigowar wannan mutum biyun watau Baita da Dominik cikin tsarin shugabancin kungiyar baiyiwa Ibrahim Canji dadi ba domin ya rage masa kafin fada aji a cikin kungiyar da yake tunkaho shine ruhinta a jihar Kano.
Wani bincike ya nuna cewa tun shigowa da kuma kama aikin wadanda mutum biyun, watau Kabiru Baita da kuma Dominik Yofa, Ibrahin Canji ya canja salo da kuma ta yin guna guni da kuma nuna halin ni ‘yasu.
Fara nuna halaye marasa kyau da Ibrahim Canji yakeyi a harkokin kungiyar sai fitowa fili sukeyi kullum, domin ko tafiya zuwa wasan kungiyar da tayi da kungiyar Kun Khalifa bai jeba kuma baaga keyarsa a wajen haduwa don tafiya wasan ba.
Wata majiyar ta tabbatarwa wannan kafa cewa kafin tafiyar kungiyar Barau zuwa wancen wasannata da kungiyar Kun Khalifa, an jira kuma, an kuma nemi shi Ibrahim Canji amma ba’aganshi ba kuma ba’aji daga gareshiba.
Kuma a lokacin da aka nemeshi ta lambobin wayoyinsa shima baayi nasarar saminshiba domin dukkanninsu a rufe suke.
Haka aka hakura aka tafi filin jirgin sama na Malam Aminu Kano don shiga jirgin sama aka kuma tafi kuma aka sami nasara ba Ibrahim Shitu Canji ba mukarrabensa. Wannan ba karamin kuskure bane domin ita maganar almindahana bafa fito da ita akayi ba har izuwa wnnan lokacin abin a cikin zargi yake.
Bincike ya nuna cewa dukkannin makarraben Ibrahim Canji dake rike da wani mikami a kungiyar kamarsu Yahaya Muhammad, daraktan wasannin kungiyar, Jabir Hassan, Technical Consultant, Abubakar Sadiq, mai kula da bangaren kasuwancin kungiyar, Umar Lawan wanda shine sakatare da kuma Isma’il Mahmoud, mai kula da walwala da jin dadin kungiyar sun juyawa kungiyar baya domin nuna biyayyarsu ga Ibrahim Canji saboda kin bin kungiyar zuwa wasanta da Kun Khalifa.
Hakika rashin zuwansu Ibrahim Canji da mukarrabensa baiyi wani tasiri ba domin a maimakon samun rashin nasara, kungiyar Barau samun nasararta ta farko tayi a kan masu masaukinsu.
Sai dai wata kafa ta bayyana mana cewa wannan rashin kyautawa da Canji da mukarrabensa sukayi bazai musu dadi ba domin kungiyar na iya tunanin ladaftar dasu.
Wannan kafa tana kira ga Ibrahim Canji da ya mukarrabensa da su canja tunani domin ita rayuwa juyawa takeyi. Ko da baa samesu laifin komi ba, bawanda zaita kasha kudinsa akan kungiya wadda ba nasara kuma ya tsaya yana kallo. Dole yayi wani abu ko hobbasa da zai kawo gyara.
A ganinmu Ibrahim Canji da mukarrabensa godewa Allah da kuma mai kungiyar yakamata suyi ba tawaye ba, domin laifin da ake zarginsu babbane kuma tunda bai fallasa ba, sai suyi shiru kuma su gyara ba yin tawaye ba.
Su sani fa, anayi da kai…