Hakika daukacin matasa da mabiya wasannin kwallon kafa na jihar Kano sunyi farin cikin kasancewar Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso a matsayin sabon kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano.
Wannan ya farune saboda matsanacin hali da harkokin wasannin suka shiga a fadin jihar nan ta Kano baki dayanta.
Da farko dai kowa yasan matsanancin halin rashin kudi dana rashin iya kyakkyawan jagoranci da mahukuntan Kano Pillars suka jefa kungiyar a ciki.
Miliyoyin bashin kudi yayiwa kungiyar kwallon kafa ta kano Pillars katutu wanda yasa masu bada bashin suka ja layi su kayi kememe suka daina bada bashin, al’amarin da ya sake jifa kungiyar Kano Pillars cikin halin ni ‘yasu a wasu likuta kadan da suka wuce.
Rigingimun ba gaira ba dalilin da shugaban kungiyar Kano Pillars ya shiga da yan kwamitin gudanarwar kungiyarma ya taimaka jeffa kungiyar cikin wasu matsalolin.
Rigingimun suna faruwane saboda mahukuntan na Kano Pillars na nemaan sanin hakikanin yadda shugaban kungiyar Kano Pillars yayi da kudaden da kungiyar ta samu wajen sayar da yan wasan da tayi da kuma hakikanin yadda akayi da miliyoyin kudin da kungiyar da samu wajen kamfanin Gongoni don Makala suna kamfanin a gaban rigunan yan wasan Kano Pillars a lokotan wasanninsu.
Haka kuma yan kwamitin kano Pillars na kuma neman sanin yadda shugaban yakeyi da miliyoyin da kungiyar take samu a lokutan wasanninta na gida.
Yakamata kuma Hon. Kwankwaso yasan cewa akwai matsala babba a hukumar wasanni ta jiha watau, Kano State Sports Commission, wanda shima ya jefa mutane matsanancin hali.
Yan watanni kadan da suka wuce hukumar ta jagoranci yan wasa da jami’en wasannin zuwa Abuja don wasannin nakasassu na kasa amma kash bayan amincewar miliyoyin kudi da gwamnati tayi musu har yau basu biya da yawa daga cikinsu hakkokin tafiyoyinsu zuwa Abujan ba.
Abin mamaki haryau babu wani takamaiman labara na yadda hukumar wasannin tayi ta miliyoyin da gwamnatti ta amince su kashe balantana su biya mutane hakkokinsu.
A jira gaba kadan…