Daruruwan mutane masu shaawar wasan kwallon kafa dake unguwar Kurna Asabe ne suka yaba da kuma godewa mai girma gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf saboda nada dan su, wan su, shuganban su da kuma abokinsu Ali Nayara Mai Samba bisa mukamin shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da yayi masa.
Dandazon mutanen sun mika wannan godiya tasu ne ga mai girma gwamna ne ta bakin jagoransu Abdullahi Adamu Jibrin a lokacin da suka ziyarci offishin wannan jaridar ta Yanar Gizo dake Kurna Asabe ranar Litinin din data gabata.
A cewar Abdullahi Adamu su fa dole su mika godiyarsu da kuma nuna jin dadi da farin cikin su bisa wanna tagomashi da mai girma gwamna yayi wa daya daga cikinsu.
Hakika munji dadin nadin da akayiwa Mai Samba saboda cancantar da yayi akan aikin da aka dora masa.
“Mun san Ali mutum ne mai kishi da son wasan kwallon kafa don haka mun san ba zai bawa mai girma gwamna kunya ba”, cewar Abdullahi Adamu Jibrin.
A karshe Malam Abdullahi ya yiwa Ali Mai Samba fatan alher da kuma bashi shawarar yin aiki tukuru don sake kafa tarihi da kuma kara martaba da kuma mutuncin yankin nasu.