Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      Celebrations as SWAN honours Ado Salisu

      October 20, 2025

      Handball: Army massacres Pillars

      October 13, 2025

      Kungiyar Barau: Kuskuren da Ibrahim Canji, mabiyansa suka tafka

      September 30, 2025

      Sauye-sayen kungiyar Barau: Kuskuren Sanata Barau tare dana Canji

      September 25, 2025

      Kano Pillars three games, one point: Stakeholders react

      September 9, 2025
    • Column

      NPFL’s unjust and unfair treatment for Kano Pillars

      October 20, 2025

      On Shehu Adamu’s assessment of Kano Pillars’ poor performance

      October 13, 2025

      SWAN: Genuine sports stakeholder than NFF, other federation members

      October 6, 2025

      Changes in Barau FC: Where DSP Barau Jibrin fumbles

      September 29, 2025

      Shehu Dikko one year in office: Is there light in the tunnel?

      September 22, 2025
    • News & Media

      Ganduje named Mi-Yetti Allah’s adviser for youth empowerment

      October 25, 2025

      Few minutes in the midst of lawyers

      October 24, 2025

      Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

      October 22, 2025

      Re-Extortion at Urology Center: Gov Abba must hear this

      October 10, 2025

      Environmental Journalists begin two-day training in Abuja

      September 23, 2025
    • Analysis

      Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

      October 22, 2025

      Technical Advisor, Assistant for Kano Pillars Suspended: What’s next for Sai Masu Gida?

      October 21, 2025

      Korar Ogenye da Yaro Yaro: Ba su suka kar zomon ba

      October 20, 2025

      Rashin kokarin Kano Pillars da Barau: Sai fa gwamnati ta yi wani abu

      October 7, 2025

      Barau FC, please wake up.

      September 15, 2025
    • Personality Profiles

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024

      Engr. Ibrahim Usman Aikawa: New Kano Poly Governing Council’s PAB’s representative

      August 24, 2024

      Aminu Kano 40 years after…

      April 17, 2024

      Ameh Agnes: A woman farmer of repute

      April 15, 2024

      Dr. Usman Ibrahim Aikawa: New Kano Poly, Director Academic Planning

      January 2, 2024
    Sports Eye
    Home » Rikita-rikitar Kano Pillars: Abinda Babangida Little ya kasa ganewa
    Sports News

    Rikita-rikitar Kano Pillars: Abinda Babangida Little ya kasa ganewa

    Sani YusifBy Sani YusifMay 13, 2024
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram

    Duk wanda ya saurari firar da gidan radiyo Arewa (Arewa Radio) yayi ranar Asabar da safe da shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Alhaji Babangida Little yayi, zai fahimta cewa Little bai fahimci shugabanci ba.

    Nayi wannan harsashene saboda yadda naji  Babangida Little yake magana a firar kamar da kudinsa na aljihunsa yake gudanar da kungiyar Kano Pillar din bba kudin gwamnai ba, domin naji shugaban yana magana da buga kirji a firar kamar wani soja ba dan siyasa ba.

    Yakamata Babangida Little ya sani cewa dan siyasa nema da jawo jamaa yake ba tarwatsa su ba. Nunawa ba wanda ya iya babban kuskurene wanda yana tare da dana sani.

    A firar naji Babangida Little na nuna cewa a wajensa yan kwamitin gudanarwar da aka nada su tare ba dole bane su san komai da zaayi a kungiyar. Wannan babban kuskure ne domin gwamnati ta nada sune suyi aiki tare.

    Idan da gwamnati so take Little yayi aiki shi kadai ba da yan kwamitin gudanarwa ba, da baza tayi  tunanin nada masa yan kwamiti ba.

    Waccan kuskurenne da ya kaishi daukar mai horarda da yan wasa Abdu Maikaba shi kadai ba tare da sahalewar sauran yan kwamitin gudanarwarba kungiyar ba yakai kungiyar Kano Pillars halin da ta sami kanta yanzu.

    Kuma shine a cewarsa ya sashi bawa Maikaba wuka da nama wajen daukar yan wasa da kuma kudin da zaa biya yan wasan da shi kansa Maikaba ba tare dda sahalewar kwamitin gudanarwarba.

    Shugaban ya fada kai tsaye shi kadai ya kawo Maikaba ba tantancewa da sahalewar yan kwamitin da gwamnati ta nadasu tare. Wannan laifine wanda yakamata gwamnati ta bincika.

    A firar tasa Little ya kuma tabbatar da cewa haka kuma zaici gaba da tsarin shugabancinsa bazai tuntubi kowa ba sai dai kawai ya sheda musu abinda yayi. Wanda wani babban kuskurenne zai sake tafkawa.

    Da kuma yake magana akan kungiyar magoya baya, Little bai nuna girmamawa garesu ba duk yasan cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da Pillars ke samu.

    Bugu da kari  yawansu da kudinsu sukeyi kuma suke kashewa don cigaban kungiyar da kuma samun nasararta.

    Nunawa magoya baya dan yatsa da Little yayi shima babban kuskurene domin zai iya sama masa rashin nasara a shugabancinsa nan gaba.

    Haka kuma, idan da tun da farko Little ya kafa kananan kwamitoci (Sub-committes) kamarsu Technical, da saurarsu a tsakanin yan kwamitin gudanarwar tasa da wasu kwararrun mutanen gari da Kano Pillars bata sami irin wannan matsalarba.

    Domin sai yan kwamitin sun gana da kuma tantance kowa zaa kawo kafin ya fara aiki ko kuma ya zama dan wasa a kungiyar. Wannan zaisa a sami gagrimar nasara domin masu hikima sunce, mai shawara aikinsa baya baci.

    A kashe, ina ganin idan har Babangida Little bai canja tsarinsa na daukar shi kadai ya iya ba, to lalle yanzu ya fara samun matsala wanda kuma ba dole guguwar ta rinka masa dadi ba.

    Allah yasa gwamnati tayi nazari ta nada masa kwararrun mutane wadanda zasuyi aiki tare kuma su sami dimbin nasara, to amma san iyawa da son kai yasa yana ta zizzille musu, to ya sani fa, irin wannan san iyawarne yake kai fara ko tururruwa bakin kadangare.

    iabinda Little ya kasa ganewa Rikita-rikitar Pillars
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleInauguration of sporting activities: Gara-Gombe invites all
    Next Article Handball competition: PS Minjibir thanks Gov Abba…assures of superlative performance
    Sani Yusif
    • Website

    I was a staff of the then Triumph Newspapers, with keen interest in sports journalism which drove me to the unit where I was supported and oiled in the dynamics of modern sports reporting by my mentor/friend, Sani Zaria, the then Group Sports Editor of the Triumph. And when he left in 1995, I tried to sustain the spirit against all odds with a column sportesye. But when The Triumph was closed, I was moved to Kano Polytechnic as a lecturer until my retirement last 3 years, which gives me time to return to what I know best , the recreation of the SPORTS EYE.

    Related Posts

    Celebrations as SWAN honours Ado Salisu

    October 20, 2025

    Handball: Army massacres Pillars

    October 13, 2025

    Kungiyar Barau: Kuskuren da Ibrahim Canji, mabiyansa suka tafka

    September 30, 2025

    Sauye-sayen kungiyar Barau: Kuskuren Sanata Barau tare dana Canji

    September 25, 2025

    Kano Pillars three games, one point: Stakeholders react

    September 9, 2025

    Gumel, Maizare, others to head newly formed SPS

    August 29, 2025
    Add A Comment

    Comments are closed.

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    Ganduje named Mi-Yetti Allah’s adviser for youth empowerment

    October 25, 2025

    Few minutes in the midst of lawyers

    October 24, 2025

    Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

    October 22, 2025

    Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

    October 22, 2025

    Technical Advisor, Assistant for Kano Pillars Suspended: What’s next for Sai Masu Gida?

    October 21, 2025
    © 2025 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.