Bayan kammala atisayen gwajin alkalen wasan kwallon kafa masu makala bajon FIFA na wata ukun farko, ofishin hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ya bayyana sunayen alkalen wasan kwallon kafa talatin da suka sami nasara.
Kwajin dai anyishine a satin da ya gabata a filin wasa na kasa mai suna Moshood Abiola National Stadium dake Abuja,
Kafin gwajin dai sai da aka fara duba lafiyar dukkannin alkalen wasan da zasu shiga gwajin don tabbatar da ingancin lafiyarsu.
Mai taimakawa babban sakataren kungiyar NFF na musamman mai kula da bangaren cigaban alkalen wasa, Mr. Mohammed Adebayo Ameenu shine ya bayyana wannan cigaba wanda mutum 30 da suka sami nasarar wanda tuni an makala musu bajinan FIFA don nuna cancantarsu.
Cikin mutane talatin da suka sami nasara akwai maza bakwai (alkalei), wasu mazan bakwai (mai taimaka), mata hudu (alkalai), wasu matan hudu (ma taimaka), mutum hudu (alkalen wasan rairayi (beach soccer)), sai kuma wasu hudun masu alkalencin wasan (5-aside) watau futsal referees.
Sanarwar ta nuna cewa daya daga cikin alkaeln wasan rairayi mai suna Jelili Ogunmuyiwa yanzu haka yana kasar Dubai wajen wasan rairayi na duniya da akeyi a Dubai.
Cikin alkalen da suka sami nasara (maza) akwai Basheer Salihu (Kano), Ogabor Joseph, Grema Mohammed, Kassim Abdulsalam, Abubakar Abdullahi, Nurudeen Abubakar da Patrick Egba
Mataimakan alkalai maza kuma akwai Igho Hope, Samuel Pwadutakam, Yakubu Mohammad, Ahmed Tijjani, Igudia Efosa Celestine, Digbori Tejiri da kuma Usman Abdulmajeed Olaide
A bangaren alkalai mata kuma akwai Hannah Elaigwu, Yemisi Akintoye, Ndidi Madu da Alaba Olufunmilayo
Mataimakan alkalai mata kuma akwai Akpan Friday Mfon, Beauty Kabenda Terah, Abibatu Yusuf da kuma Faith Agbons
A bangaren wasan kwallon rairayi kuwa akwai Ahmed Rabiu (daga Kano), Ogunmuyiwa Jelili, Fawole Olawale da kuma Olayinka Olajide.
Alkalen wasan rairayi akwai Musa Dung Davou, Paul Umuago, Ukah Ndubuisi da kuma Bello Zuru.