Hakika ganin yadda kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ke ta tabarbarewa ya zama dole a nutsu sosai don samo bakin zaren da ya tsunduma kungiyar cikin wannan halin na ni ‘yasu.
Wasu na ganin cewa ruguza shugabancin kungiyar da maye gurbinsu da wasu shine a’ala amma ko kadan wasu naganin hakan ba shi bane mafita.
Masu da’awar rushe shugabancin kungiyar na nuna sakaci da shugabannin sukayi wajen nemo zakakuren yan wasa da zasu cike gurbin wadanda suka tsufa ko kuma sauya kungiyoyi.
Wasu kuma na ganin cewa shi wannan al’amari rubutaccene don haka kowa aka kawo kome kyaunsa babu yadda ya iya haka zaa gani.
Amma wani bincike da muga gudanar ya nuna cewa ita kungiyar Kano Pillars nada alhakin mutane da yawa a wuyanta wanda kuma ana ganin wannan hakin na mutane da ta kasa saukewa na iya binta ya kuma daureta ta kuma kasa komai.
Bincike ya nuna cewa mutane da dama na bin kungiyar Kano Pillars miliyoyin kudade da wasu rantarsu akayi don gudanar da ayyukan kungiyar wasu kuma ladan aikine wanda baa biya ba kuma babu ranar biyan.
Alal misali kowa yasan a lokacin shugabancin Babangida Little, an karbi miliyoyin kudi kimanin miliyan saba’in (N70m) a wajen Alhaji Naziru Wapa don tafiye-tafiyen kungiyar amma haryau baa zancen yadda zaa rage masa bashin balantana a biya shi kudinsa.
Akwai kuma labarin cewa tsohon mai horarda kungiyar mai suna Ibrahim Jugnu ma yana bin kungiyar bashin miliyoyin kudi wanda shima baa fara tunanin biyansa hakkinsa ba.

Ko mai horarwa na kwana kwanannan watau Usman Abdallah ya bayyana cewa shima da haakkinsa akan kungiyar wanda duk da an sallameshi, baa biyashi ba.

Uwa uba akwai miliyoyin kudin da tsohon sakataren kungiyar Kano Pillars watau Bashir Maizare ya bayar don gudanar da ayyukan kungiyar, amma har yanzu baa maganar kudin balle a fara tunanin biyansu.

Bincike ya nuna akwai mutane da dama wadanda tsofaffin shugabannin kungiyar da siuka shude suka ranci ko kudi ko anshi kayansu amma har yanzu biya ba labara.
Haka kuma bazai zama abin mamaki ba idan akace tsohon mai horar da kungiyar na baya bayannan watau Evans Oginye nada hakki akan kungiyar wanda basu bashi ba. Babu mamaki idan akace Abdu Maikaba nabin kungiyar bashi.

Amma ya zama dole a yabawa mai girma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf saboda biyan iyalen marigayi Salisu Yaro bashin miliyoyin kudin da yakebin kungiyar Kano Pillars kafin rasuwarsa.

Mu tuna alhaki kwikwiyo ne, bin mai shi yake.
