Daga MUSA HASSAN KURNA
Wannan tambayar “Ta yaya muka sami kanmu a haka?” ita ce tambayar da yawancin masoya kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suke yi yau, a wani lokaci da kulob ɗin da a baya ya saba zama abin alfahari ga mutanen Kano kadai ba har da na Arewacin Najeriya gaba ɗaya.
Ita wannan tambayar tana neman amsar yadda Kano Pillars ta sami kanta a wannan hali duk da tagomashin da take da shi a wajen magoya baya da masu kallo.
A gaskiya, wannan koma-bayar ba ta faru cikin dare guda ba. Domin bincike ya nuna matsalolin Pillars sun samo asali ne daga tarin matsaloli da aka bari suna girma, wasu daga cikinsu na cikin gida ne, wasu kuma na tsarin gudanarwa gaba ɗaya.
Ga manyan abubuwan da suka jawo muka tsinci kanmu a wannan yanayi:
- Rashin tsari da ci gaba mai dorewa
Pillars na da tarihi, suna, da masoya. Amma shekaru da yawa babu cikakkiyar hanya mai dorewa ta: gina ƙungiyar matasa, tsare tsaren horo da tabbatar da ci gaba ko sakamakon da ya daure. Kungiyar Kano Pillars ta dogara da sunanta, ba tsarin aiki mai dorewa ba.
- Sauya koci da ’yan wasa ba tare da tsari ba
Kowanne lokaci ana canje-canjen masu horararwa da yan wasa, amma ba tare da bin wata manufa ta tsawon lokaci ko tsarin sake gina ƙungiyarba. Wannan ya haifar da rashin daidaito, rashin fahimtar juna tsakanin ’yan wasa, masu horar dasu, da kuma rashin kwanciyar hankali.
- Matsalolin gudanarwa da rashin ingantaccen jagoranci
Babban mummunan tasiri shi ne: rashin gaskiya da tsari a tafiyar da kulob, cusa siyasa cikin al’amuran ƙungiya da watsi da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki masu kishin kulob.
Inda babu jagoranci mai hangen nesa, babu sakamako mai kyau.
- Rashin amfani da damar da ake da shi
Pillars na da masoya da goyon baya da yawa fiye da kusan dukkan kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya. Amma ba wata kafa ta saurararsu.
Abinda gwamnati taga dama shi kawai takeyi. Wannan shine ra kawo abubuwa kamar har: ba a saka jari a kayan aiki, ba a inganta harkar kasuwanci (marketing) ga kuma babu ingantaccen scouting na sabbin ’yan wasa.
- Rashin ɗaukar darasi daga matsalolin baya
An yi kuskure iri ɗaya shekaru da dama akan rikicin kujeru, dakatarwa, faduwa form, koma-baya a gida, amma babu wani tsarin hukunci ko gyaran da ya hana maimaituwa.
A ƙarshe: Ta yaya muka sami kanmu a haka? Saboda mun bari ƙungiya da tarihi ta faɗa hannun sakaci, rashin tsari, da jagoranci mara inganci. Mun dogara da tarihin Pillars maimakon mu gina makomarta.
Hassan Kurna mazauni Kurna Asabe ne.
