Mun sami labarin cewa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na bukatar addu’a domin a yanzu haka suna Agbo Junction manyan motocin sun tare hanya sakammakon wata babbar mota data kife a kan hanya.
Kano Pillars na kan hanyarta na zuwa jihar Bayelsa don wasanta da kungiyar Bayeksa United.
A cewar Media Officer na kungyar Sharif Kofar Nasarawa a yanzu haka suna dab da Benin Edo state a makale.
Wannan yasa motocin kungiyar Kano Pillars makalewa cikin Manyan Motoci Bagaba Ba Baya.
Don haka a bukatar adduar kowa da kowa don samun mafita.
Allah ya kai musu dauki ameen.