Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      NFF names Mahmud Hadejia chairman of Beach Soccer, Futsal committee

      July 14, 2026

      New Kano Pillars Management: Any hope for real change?

      July 13, 2026

      Gombe Emir’s Cup: Organisers unveil quarter-final fixtures, match dates

      July 10, 2026

      Gombe Emir’s Cup Quarter-Finals set as Eight Clubs progress

      July 8, 2026

      Babangida takes helm of Kano State Sports Commission

      July 6, 2026
    • Column

      Has Barau FC management lost sight of Senator Barau’s vision?

      July 24, 2026

      Free transfer blow: Should Kano Pillars have let Fabian Nworie leave for nothing?

      July 17, 2026

      With full government support, Babangida, Maizare, others must produce results

      July 10, 2026

      Gov. Abba’s listening approach: Key to reviving Kano Pillars, Kano Sports Commission

      July 3, 2026

      Kano State Sports under siege: Governor Abba must hear it

      June 26, 2026
    • News & Media

      Keyamo, Musawa confirmed as speakers for 9th National Tourism Transportation Summit & Expo 2026

      July 24, 2026

      Keyamo, Musawa Confirmed as speakers for 9th National Tourism Transportation Summit & Expo 2026

      July 24, 2026

      Katsina Government seeks Kano’s expertise to establish Culture, Reorientation Agency

      July 15, 2026

      NTDA partners Ringo Sport Club for NISPRISPORT 2026

      July 15, 2026

      NASTOCE 2026: Chief Abiodun Odusanwo, Dr. Badaki Aliyu Earn Meritorious Honours

      July 14, 2026
    • Analysis

      Kano Sports: Huge expectations for new Kano Pillars, Sports Commission Boards

      June 29, 2026

      Kano Pillars’ survival hopes alive despite tough battle ahead

      May 22, 2026

      NPFL survival at stake: Relegation battle heads into final day

      May 14, 2026

      Kano Pillars: Final words before crucial Plateau United FC encounter

      May 12, 2026

      Alleged Bias in Kano Sports Support: What Kano FA Should Address

      May 5, 2026
    • Personality Profiles

      Engr. Aikawa assumes Office as pioneer Deputy Rector (Academics)

      July 6, 2026

      Making of a Leader: Dr. Garba A. Adamu’s journey from laboratory to leadership

      July 4, 2026

      AbdulGaffar I. Dawakin Tofa: Shaping public discourse through journalism, broadcasting

      June 24, 2026

      Muhammad Wasilu Kawo: New Nasara Radio Program Manager

      December 19, 2025

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024
    • Advert Rates
    Sports Eye
    Home » Hana yan tawagar wasannin nakasassu hakkinsu: A ina aka kwana ne?
    Sports News

    Hana yan tawagar wasannin nakasassu hakkinsu: A ina aka kwana ne?

    Sani YusifBy Sani YusifMarch 18, 2024
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram

    Yau  wata uku cif da zuwa da dawowar yan wasan jihar Kano daga wasan kasa na nakasassu watau (2023 National Para-Games Competition) wanda akayi a Abuja amma har yanzu hukumar wasanni ta jihar Kano (Kano State Sports Commission) bata biya mafi yawancin yan tawagar zuwa Abujan hakkokinsu ba (Daily Travelling Allowances).

    Wani abin haushi datakaici wanda kuma ya zubarwa da hukumar wasannin ta jihar Kano mutunci a idon jamaa shine kasa wani katabus don karbowa mafi yawancin yan tawagar hakkokinsu daga gwamnati kamar yadda suke cewa.

    Bincike ya nuna mummunar wahalar da dukkannin yan tawagar jihar Kano suka sha a lokacin da suke Abuja gabadayansu saboda rashin biyansu alawus din da yakamata a basu tun kamin tafiyar tasu zuwa babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.

    Idan bamu manta ba, hukumar wasan ta jihar Kano ta tura yan wasa, masu horar dasu, sakatarorin tsare-tsare, likitoci, yan jarida, direbobi, jami’en tsaro da sauransu zuwa Abuja ba tare da basu kudaden alawus dinsu ba (DTA) da alkawarin damka musu kudadensu da sun isa Abuja.

    Amma wani abin takaici da suka isa Abuja sai hukumar wasannin tayi musu kememe al’amarin da ya jefa dukkannin yan tawagar cikin rudani da dimuwa saboda tsanani rashin kudi da suka shiga.

    Wannan ya faru ne saboda mafi yawancinsu basu da kudin cin abinci balantana na inda zasu kwanta ga shi kuma basusan kowa a Abuja ba. Ga kuma rashin kudin sufuri daga can zuwa can.

    Da wuya tayi wuya sai suka koka ta hanyar yan jaridun da suke tare dasu wanda yasa mukaddashin hukumar wassannin ta jihar Kano, Malam Bala Malam magantuwa.

    A jawabinsa ga yan jarida Malam Bala ya bayyana karbar Naira miliyan tara (N9m) cikin miliyan 30 da suka nema daga gwamnati wanda kuma a cewarsa yayi amfani da kudin ya biya kudin rijistar yar wasa al’amarin ya rudarda jama’a da dama.

    A wancen lokacinne Malam Bala yayi alkawarin biyan kowa alawus dinsa da zarar sun komo gida jihar Kano.

    Bincike ya nuna mafiyawancin yan tawagar mutanene masu iyali kuma sun bar gida da alkawarin da sun isa Abuja zasu turowa iyalensu kudin kashewa wanda rashin biyan ya jefasu cikin wata dimuwar.

    Wani  abin haushi kuma shine da suka komo gida alkawarin bai cika ba domin mukaddashin shugaban hukumar yayi biris da maganar, al’amarin da yasa yan tawagar kara magantuwa ta kafafaen yada labarai masu dama.

    Wannance ta firgita shi inda yaje ya samo kudi amma kash a maimakon ya biya dukkannin yan tawagar sai ya zabi wasu a cikinsu har da yan jarida ya biya ya kuma manta da sauran. Al’amarin da jama’a da dama sukayi Allah wadai da kuma kokarin toshe bakin masu magana wanda yayi nasara.

    Wani karin abin takaicin kuma shine cikin mutanen da Malam Bala yaki biya akwai likitoci da dirobobi wadanda arosu akayi daga wasu ma’aikatu don su taimaka a sami nasarar tafiyar.

    Bugu ga kari  su kuma sauran kamarsu sakatarori su suke samo masu horarwa sannan su kuma masu horarwa su samo yan wasa.

    Amma ya biya yan wasa ya manta da sakatarori da masu horarda yan wasan wanda shima babban koma bayane.

    A ganina biyan wasu yan wasa da kuma kin biyan wadancen jami’en ba daidai bane kuma ya nuna rashin sanin aiki da kuma rashin iya gudanarwa.

    A nan nake tunawa Malam Bala yadda ya karbo naira miliyan tara ta farko daga cikin miliyan talatin da gwamnati ta amince a kasha da kuma kudin ya kara  amsowa wadanda bamusan yawansu ba ya biya wasu yan wasa da yan jarida, yakamata ya yi namijin kokari wajen nemo sauran kudaden ya biya masu hakki hakkinsu.

    Yakamata Malam Bala ya sani cewa shi shugabanci ba zama ko iya zama a ofis bane. Yin abin da yakamata a lokacin da yakamata shine shugabanci.

    Yin shiru ba gwaninta bane domin a watan goma sha daya za a sake wani wasan, da wane ido ko fuska zaa kara neman wadannan mutanen don samun gudummawarsu?

    Bugu da kari, shugaban hukumar wassannin yakamata ya  sani cewa da wadannan mutanen da bayaganin kimarsu da mutuncinsu basu agazaba, da tafiyar zuwa Abuja bata yiwu ba

    Tun da har mai girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince a biya banga dalilin da Malam Bala zai rinka baya-baya ba. Ya tashi ya je inda ya kamata don karbowa mutane hakkinsu.

    Ya kuma kamata Malam Bala ya fara amfani da kudaden shiga da hukumarsa take samu daga sitadia ta Sabon Gari da ta Kofar Mata da kuma filin wasa na Ado Bayero Squre don fara rage kudin kafin ya amso wadancan.

    Hakkinsu Hana yan tawagar wasanni
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleJamaa, asa Kano Pillars cikin addua
    Next Article Pain and gain of a writer
    Sani Yusif
    • Website

    I was a staff of the then Triumph Newspapers, with keen interest in sports journalism which drove me to the unit where I was supported and oiled in the dynamics of modern sports reporting by my mentor/friend, Sani Zaria, the then Group Sports Editor of the Triumph. And when he left in 1995, I tried to sustain the spirit against all odds with a column sportesye. But when The Triumph was closed, I was moved to Kano Polytechnic as a lecturer until my retirement last 3 years, which gives me time to return to what I know best , the recreation of the SPORTS EYE.

    Related Posts

    NFF names Mahmud Hadejia chairman of Beach Soccer, Futsal committee

    July 14, 2026

    New Kano Pillars Management: Any hope for real change?

    July 13, 2026

    Gombe Emir’s Cup: Organisers unveil quarter-final fixtures, match dates

    July 10, 2026

    Gombe Emir’s Cup Quarter-Finals set as Eight Clubs progress

    July 8, 2026

    Babangida takes helm of Kano State Sports Commission

    July 6, 2026

    Sports sector reforms: National Sports Commission earns ABU’s praise

    July 6, 2026
    Add A Comment

    Comments are closed.

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    Keyamo, Musawa confirmed as speakers for 9th National Tourism Transportation Summit & Expo 2026

    July 24, 2026

    Keyamo, Musawa Confirmed as speakers for 9th National Tourism Transportation Summit & Expo 2026

    July 24, 2026

    Has Barau FC management lost sight of Senator Barau’s vision?

    July 24, 2026

    Free transfer blow: Should Kano Pillars have let Fabian Nworie leave for nothing?

    July 17, 2026

    Katsina Government seeks Kano’s expertise to establish Culture, Reorientation Agency

    July 15, 2026
    © 2026 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Advert Rates
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.