Daga Ahmad Abdul Fatakwal
Bayan shafe wasu shekaru ana cin kasuwar dare a unguwar Hausawa dake birnin
Kalaba fadar Gwamnatin jihar kuros riba
Kasuwanci na kara fadada musamman a kasuwar dare wacce ta fara kamar da wasan yara wanad a yanzu sai qara bunkasa take.
Kasuwar na fara ci tun daga kusa da fara sallar magariba har izuwa karfe tara na dare kullum.
Wakilinmu da ya ziyarci kasuwar yammacin kwanan baya ya tarar da kasuwar na tsaka da hada hada ana ta saye da sayar.
A kasuwar akwai takalman sanyawa kala daban daban da suka hada dana yara, manya dana ‘yan makaranta.
Da yake zantawa da Yusuf Miga, shugaban ‘yan kasuwar, ya shaidawa wakilin mu cewa ‘ya fara tsugunnwa a gefen hanya da ‘yar Lema a lokacin da yake sayar da takalma wanda idan ruwa yazo sai ya kwashe ko kuma ya rufe su da leda ya kuma koma gefe don ya fake ruwa musamman idan ana yin ruwan sama.
Yaci gaba da cewa “Takalma kala daban-daban nake sayarwa akwai kuma na yara da kuma na masu zuwa motsa jiki da kuma na masu buga kwallom kafa.
A kasuwar dake ma’adanar man Fetur kuma kuwa da wakilinmu ya leka, akwai masu sayar da abinci ko wane iri musamman idan mutum daga Arewacin Najeriya ya fito.
Haka kuma a kasuwar akwai masu sana’ar sayar da magunguna, kayan gwanjo da sauran kayayyaki da ake amfani dasu na yau da kullum.
A kasuwar dabbobi kuwa, akwai awakai, shanu da raguna saboda masu bukata.
A unguwar Hausawa kuwa akwai masu sana’ar sayar da ruwa wato ‘Yan Garuwa wanda Salisu Bako an sami canji sosai a harkar.
A bangaren masu abinci kuwa, wakilin namu ya rawaito sun kara farashi tuwo da kuma sauran abinci irin na mutanen arewa.