Wani babban mutum wanda kuma tsohon dan jarida ne mai mikamin edita ya turomin wani fefan vidiyo mai cike da abin haushi da takaici.
Shi fefan vidiyon ga dukkan alamu a filin wasan kwallon kafa kuma na Arewacin kasarnan aka daukeshi kuma a lokacin wasa.
Babu wani abin birgewa ko sha’awa idan mutum ya kalla kuma ya saurara domin ashariyace kawai ake tayi da taimakon wani makadi.
Abin tambaya yaushe anan shine, yaushe Bahaushe wanda aka sani da addini da sanin yakamata ya samo wannan mummunar dabi’ar ta hangame baki dayin ashariya haka?
Ta yaya mu da muke jama’ar Manzon tsira Annabi Muhammad (SAW) muka zunduma cikin irin wannan mummunan hali na rashin da’a da sanin yakamata?
Kowa yasan wajen kallon wasan kwallon kafa ba waje bane na nuna irin wannan mummunar dabi’ar amma wajene na nishadi da hutawa.
Don haka ina kira ga kungiyoyin magoya bayan kwallon kafa da su san abinda yakamata suyi kuma susan irin goyon bayan da yakamata su rinka yiwa kungiyoyinsu.
Shigowa da makadi mai kidan batsa ko ashariya cikin filin wasa kawai da sunnan goyon baya ba daidai bane kuma bai kamata ba.
Yakamata suma shugabannin kungiyoyin kwallon kafa susa baki wajen ganin an dakatar da wannan mummunar dabi’ar wadda taci karo da al’adunmu da kuma addininmu.
A ganina babu laifi idan magoya baya ko shugabanni kungiya su kawo masu kida cikin filin wasa, amma susan irin kida da wakar da zasuyi ba na zagi ko ashariyaba.
Yakamata mu sani cewa, ba a san bahaushe da ashariya ba balantana cin zarafin wani.
A madadin irin wadannan wakokin na batsa da rashin kunya da badala, ina kira ga wadanda abin ya shafa da su duba irin yadda turawa sukeyi don a samo bakin zaren.
A ganina, a iya sa wakokin (recorded) a loudspeakers na stadium dan su dinga karawa ‘yan wasan kuzari da kuma nishadantar da yan kallo kamar dai yadda akeyi a Turai.
Anan ina kira ga shugabannin Kano Pillars dana sauran kungiyoyin kwallon kafa na arewacin kasarnan musamman jahohin musulmi da su nemi marubuta wakokin hausa don su rubuta da kuma rera wakokin karfafa gwiwa masu ma’ana ba na ashariya ba.
Zunduma ashariya ba hali da al’adarmu bace.