Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      A sake tunani: Ruguje shugabancin Kano Pillars ba mafita bane…

      November 10, 2025

      Anya ba hakkin yan wasa da ma su horaswa ke bin Pillars, Barau ba?

      November 6, 2025

      NUGA Games: Northwest Varsity Departs, Poised for Excellence

      November 5, 2025

      Canjin shugabannin Kano Pillars: Ba shi bane mafita

      November 5, 2025

      Korar Yaro Yaro a Pillars: Menene laifin sa?

      November 3, 2025
    • Column

      My Reflections on Adamu’s Kano Pillars’ poor performance views

      November 10, 2025

      Fitness Test: Over 1,500 Referees, Assessors to converge in Kano ‘morrow

      November 7, 2025

      NPFL: Can Kano Pillars stand test of time?

      November 3, 2025

      TSY: Accomplished talent scout, content producer, football agent

      October 27, 2025

      NPFL’s unjust and unfair treatment for Kano Pillars

      October 20, 2025
    • News & Media

      70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Ibrahim Shekarau

      November 5, 2025

      70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Shekarau

      November 5, 2025

      Happy birthday, Magistrate (Coach) Ibrahim Gwadabe

      November 3, 2025

      Kidney Patients send SOS to Governor AKY

      October 29, 2025

      Ganduje named Mi-Yetti Allah’s adviser for youth empowerment

      October 25, 2025
    • Analysis

      Matsalar Kano Pillars ibtala’ice, amma…

      October 28, 2025

      Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

      October 22, 2025

      Technical Advisor, Assistant for Kano Pillars Suspended: What’s next for Sai Masu Gida?

      October 21, 2025

      Korar Ogenye da Yaro Yaro: Ba su suka kar zomon ba

      October 20, 2025

      Rashin kokarin Kano Pillars da Barau: Sai fa gwamnati ta yi wani abu

      October 7, 2025
    • Personality Profiles

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024

      Engr. Ibrahim Usman Aikawa: New Kano Poly Governing Council’s PAB’s representative

      August 24, 2024

      Aminu Kano 40 years after…

      April 17, 2024

      Ameh Agnes: A woman farmer of repute

      April 15, 2024

      Dr. Usman Ibrahim Aikawa: New Kano Poly, Director Academic Planning

      January 2, 2024
    Sports Eye
    Home » Rashin kokarin Kano Pillars da Barau: Sai fa gwamnati ta yi wani abu
    Sports Analysis

    Rashin kokarin Kano Pillars da Barau: Sai fa gwamnati ta yi wani abu

    Sani YusifBy Sani YusifOctober 7, 2025
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram
    1aa

    Hakika gwamnati a cikin rayuwa da harkokin jama’arta yar kallo ce. Sai da babban aikinta shine sa ido da kuma samar da tsarirrika da yanayi wanda jama’arta zasu sami damar tafiyar da harkokinsu a sauwake cikin lumana.

    Gwamnatoci na samun kwanciyar hankali da kuma gudanar da mulkinsu a saukake, idan sun fuskanci jama’arsu na da abinyi kuma harkokinsu na wanzuwa ko tafiya daidai ba cuta ba kuma cutarwa.

    Kowa ya sani ba aikin gwamnati bani shiga harkokin kasuwanci ko makamancinsu, a’a, aikin gwamnati shine samarda da yanayin yin kasuwancin ko wasu muhimman harkoki na halas da kuma tsaro dan komi ya tafi daidai.

    Amma yana zama wajibi a wasu lokutan gwamnati ta tsunduma kanta cinki harka musamman idan ta duba cewa jama’arta na da shaawa ko muradin wannan harka amma babu masu gudanarwa ko zuba jari a cikinta.

    Irin wannan dalilinne yasa gwamnatocin kasar nan da dama ke tsuduma cikin harkar mallakar kungoyin wasanni kamar kwallon kafa, kwallon kwando, kwallon raga da sauransu.

    Alal misali a Maiduguri gwamnatin jihar Borno ke daukar nauyin kungiyar kwallon kafa ta El-Kanemi, a jihar Pilato, gwamnatin jihar ke da Plateau United, a jihar Kwara, akwai Kwara United, a jihar Rivers, gwamnatin jiharce ke daukar nauyi Rivers United, sai nan Kano inda gwamnatin jihar Kano ceke  daukar nauyin  kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars haka kuma sauran jahohi.

    Gwamnatocin jahohi na daukar nauyin wadannan kungiyoyin wasanne saboda rashin samun shigar yan kasuwa ko kungiyoyin da ba na gwamnati ba shiga harkar saboda makudan kudin da harkar ke ci sannan kuma babu wata tabbatacciyar riba  a ciki.

    Da akwaimasu daukar nauyin irin wadaannan kungiyoyi, to fa babu yadda gwamnatocin jihohi zasu tsunduma kansu cikin harkar, saidai kallo kawai.

    Don haka tunda a yanzu a Kano an sami mutane daidaiku suna nuna shaawarsu wajen daukan nauyin ko mallakar kungiyoyin wasan kwallon kafa a jihar Kano, to fa zama wajibi ga gwamnatin jiha to fito fili ta taimakawa kungiyoyin don samun nasararsu.

    Wajibcin  hakan ya faru ne saboda damar da yawacin matasan jiharnan suka samu na damar yin wasan a kungiyar Barau ba tare da sun je ko’ina ba.

    Bugu da kari jama’ar gari ma sun sami wata damar na kasha kwarkwatar idanunsu wajen ganin manya kungiyoyin wasan kwallon kafa na wasu jahohi.

    A halin yanzu, matsayin kungiyoyinmu biyu masu daraja, watau Kano Pillars FC da Barau FC dake cikin  gasar Nigeria Premier Football League (NPFL) sun zama abin damuwa ga masoya, ‘yan wasa da masu ruwa da tsaki a harkar wasanni a fadin Jihar Kano da ma kasa baki daya.

    Wadannan kungiyoyi biyu, wadanda a da suke alfahari da daukaka ga jama’ar Kano, yanzu suna fama da rashin nasara tare da kasancewa a kasan teburin gasar, lamarin da ke bukatar gaggawar kulawa daga gwamnati.

    A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa Barau FC na da maki biyar kacal, yayin da Kano Pillars FC ke da  hudu, abin da ke nuni da tabarbarewar da ta samo asali daga rashin kyakkyawar tafiyar da al’amuran gudanarwa da kuma matsalolin fasaha.

    Magoya baya sun dade suna jimami da takaici yayin da suke kallon kungiyoyinsu nata rashin nasara a gasar duk da tarihin Kano na kasancewa cibiyar hazikan ‘yan wasa da kwarewa a harkar kwallon kafa.

    Bincike da lura sun nuna cewa akwai wasu muhimman dalilai da suka haddasa wannan tabarbarewowin:

    1. Rashin Kyakkyawar Gudanarwa: Babu isasshen kulawa da tsari tsakanin shugabancin kungiyoyin da hukumomin gwamnati masu kula da harkar wasanni.
    2. Rashin Kudi da Tsarin Amfani da Albarkatu: Kungiyoyin suna fama da karancin kudi ko kuma rashin tsari wajen kashe kudade, da kuma matsalar kulawa da ‘yan wasa, wanda ke rage musu kwarin gwiwa.
    1. Matsalar Koyarwa da Horarwa: Sauyawa a fannin masu horarwa da rashin tsayayyen tsarin fasaha suna hana kafa daidaitaccen tsari na dogon lokaci.
    1. Rashin Zuba Jari a Matasa: An kasa baiwa matasa dama ta shiga cikin kungiyoyi ta hanyar horarwa daga matakin ƙasa, lamarin da ke sa kungiyoyi su dogara da siyan ‘yan wasa na wucin gadi.
    1. Rashin Tsari da Binciken Ayyuka: Rashin bin diddigin aikace-aikace da rashin gaskiya a cikin tsarin gudanarwa ya jawo watsi da nagarta da sakaci.

    Don dawo da martaba da nasarar kungiyoyin, ina bada wadannan shawarwarin ga Gwamnatin Jihar Kano da masu ruwa da tsaki:

    1. Kafa Kwamitin Bincike Mai ‘Yanci: Gwamnati ta nada kwamitin kwararru da tsofaffin ‘yan wasa, masu gudanarwa, da wakilan magoya baya domin yin cikakken bincike kan yadda ake tafiyar da Pillars da Barau FC.
    1. Yi Binciken Kudi da Gudanarwa: A gudanar da cikakken binciken kudade da tsarin gudanarwa domin gano kura-kurai da daukar matakin gyara.
    1. Tsarin Sabon Gudanarwa: A kafa sabon tsari na gudanarwa wanda zai kasance mai zaman kansa amma na gaskiya da amana, tare da sakamako bisa aiki da nagarta.
    1. Zuba Jari a Matasa da Harkar Gargajiya: A farfado da kungiyoyin matasa da cibiyoyin horaswa domin samar da sabbin ‘yan wasa masu kwarewa daga Kano da kewaye.
    1. Kafa Shugabannin Fasaha Masu Kwarewa: A nada koci da jami’an fasaha masu kwarewa tare da tabbatar da suna da kwangila da sharuddan aiki bisa nasarori.
    1. Gwamnati Ta Kara Kula da Bin Didddigi: Duk da karfafa hadin gwiwar masu zaman kansu, gwamnati ta ci gaba da sa ido don tabbatar da cewa duk kudade da kayan aiki suna zuwa ga manufar ci gaban kungiyoyin.

    Martabar Kano a fagen kwallon kafa tana cikin barazana saboda irin wannan tabarbarewa.

    Lokaci ya yi da Gwamnatin Kano ta dauki mataki cikin gaggawa domin dawo da karfin gwiwa, kwarjini, da sahihancin gudanarwa a Kano Pillars FC da Barau FC.

    Idan aka dauki matakai cikin hikima yanzu, wadannan kungiyoyi za su sake zama tushen farin ciki, hadin kai da ci gaban tattalin arziki ga al’ummar Jihar Kano da Najeriya baki daya.

    Haka kuma yakamata gwamnati ta sani cewa barin su wadannan kungiyoyin a haka babbar illace ga jihar Kano a fagen wasan kwallon kafa.

    A fidda siyasa, a kuma duba jihar Kano da kuma cigaban jihar kawai.

    Barau Dole gwamnati Kano Pillars Kokarin Rashin tayi wani abu
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleSWAN: Genuine sports stakeholder than NFF, other federation members
    Next Article Extortion at Urology Center: Gov Abba must hear this
    Sani Yusif
    • Website

    I was a staff of the then Triumph Newspapers, with keen interest in sports journalism which drove me to the unit where I was supported and oiled in the dynamics of modern sports reporting by my mentor/friend, Sani Zaria, the then Group Sports Editor of the Triumph. And when he left in 1995, I tried to sustain the spirit against all odds with a column sportesye. But when The Triumph was closed, I was moved to Kano Polytechnic as a lecturer until my retirement last 3 years, which gives me time to return to what I know best , the recreation of the SPORTS EYE.

    Related Posts

    My Reflections on Adamu’s Kano Pillars’ poor performance views

    November 10, 2025

    Canjin shugabannin Kano Pillars: Ba shi bane mafita

    November 5, 2025

    NPFL: Can Kano Pillars stand test of time?

    November 3, 2025

    Matsalar Kano Pillars ibtala’ice, amma…

    October 28, 2025

    Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

    October 22, 2025

    Technical Advisor, Assistant for Kano Pillars Suspended: What’s next for Sai Masu Gida?

    October 21, 2025
    Add A Comment

    Comments are closed.

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    What do we really want as Nigerians?

    November 12, 2025

    A sake tunani: Ruguje shugabancin Kano Pillars ba mafita bane…

    November 10, 2025

    My Reflections on Adamu’s Kano Pillars’ poor performance views

    November 10, 2025

    Fitness Test: Over 1,500 Referees, Assessors to converge in Kano ‘morrow

    November 7, 2025

    Anya ba hakkin yan wasa da ma su horaswa ke bin Pillars, Barau ba?

    November 6, 2025
    © 2025 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.