Hakika magoya baya da masu bibiyar harkokin wasanni ba a Kano ba kawai harma da arewacin kasar nan koma  fiye da hakan sun yi farin cikin sanarwar da kwamishinan wasannin jihar Kano, Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso ya bayar game da rushe shugabancin hukumar riko na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars karkashin shugabancin Alhaji Babangida Little a makon da ya gabata.

Wannan ya biyo bayan rashin iya gudanar da shugabanci da shugaban hukumar kwallon kafan Kano Pillars din, Alhaji Babangida Little ya ta nunawa tun lokacin da aka nada shi a matsayin shugaban kwamitin har zuwa ranar da aka  rusa su.

Babangida Little ya kasa fahimtar aikinsa dana yan kwammitin gudanarwarsa da gwamnati ta nada masa donyin aiki tare don haka yata rikita-rikita da baragada har ta kaishi ga wannan hali.

Kowa yasan tun ranar da aka nada shi da yan kwamitin gudanarwarsa, Babangida Little ya shata  layin boye-boye da kiyayya tsakaninsa da yan kwamitin gudanarwar kungiyar.

Little ya kama kallon yan kwamitin nasa a matsayin abokan gaba bana aiki ba don haka  yasashi komawa koma gefe yana ta ayyukan gudanar da kunkiyar Kano Pillar aboye shi kadai ba tare do ko sanin yan kwamitin gudanarwarba.

Komawarsa gefe yasa ya tayin aiki da zartar da abubuwa iri-iri shi kadai ba tare da sani ko amincewar yan kwamitin gudanarwa kungiyar ba.

A lokacin da yake aiki shi kadai tilo, Little ya dauki masu horarda yan wasan kungiyoyin Under-15, Under-17 da na Junior Pillars na Kano Pillars din da kuma yi musu albashi ba tare da bakin yan kwamitin ba.

A wacen lokacin anyi zargin sayarda yan wasan Kano Pillars da dama ba tare da sanin su yan kwamitin gudanarwar kungiyarba.

Wannan ta sa yan kwamitin sanarda mai baiwa gwamna shawara akan wasannin, Hon. Ogan Boye halinda da ake ciki don  sasantawa amma abin yaci tura tunda shi Little  gani yake yafi kowa kuma yafi kowa sanin harkar.

Koda yake Ogan Boye yayi kokarin nunawa Little mahimmancin tafiya dayan kwamitin kungiyar, bincike ya nuna Little  bai saurareshi ba dommiin abin gaba yayi balantana ya ragu.

Ana cikin wannan tataburzar sai wani rikicin ya barke tsakanin Little dayan kungiyar magoya bayan Kano Pillars saboda nuna rashin jin dadinsu da yadda yake gudanar da harkokin kungiyar.

Wannan tasa Little juya musu baya da kuma nuna musu su ba komai bane a harkar wanda ya hargitsa da kuma tunzura su don su a ganinsu da kudin su sukeyin harkar ba kudin kowa ba.

Ta kai cewa  idan Kano Pillar na  wasa a waje watau (away) idan suka biya kudinsu suka je garin da Pillars din zatayi wasan, Little baya nuna farin cikinsa da ganinsu ko kuma yi musu maraba balle sannu da  zuwa.

Kwatsam sai aka sami labarin Little ya kulla alakar kasuwanci da kamfanin Gongoni masu yin RAMBO shi kadai ba tare  da sanin kowa ba.

Wannan shima ya hargitsa hazo inda aka ta kira da a fadi abubuwan da alakar ta kunsa wanda har yau wai wai kawi akeji domin ba wanda yasan hakikanin kudin da kamfani suka baya Kano Pillars.

Rashin tabbas da boye-biyen da Little ya keyi a wancen lokacin yasa kungiyar shiga wani hali inda ta ta rasa nasara a wasanninta na gida da waje, al’amarin da yasa kungiyar komawa kasa sosai a table.

Wand kuma yasa kungiya magoya bayan Kanno Pillars suka kira taro a cibiyar yan jaridu don neman  mafita.

A wannan taron mai horar da  yan wasan kungiyar, Abdu Maikaba  ya fito da abin boye fili a inda ya fadi dalilan rashin nasarorin kungiyar a wasannin da suka gabata.

Jin wadancen maganganu na Abdu Maikaba, Little sai kuma ya dora kahon zuka ga shi Maikaba inda ya sanarda dakatar da Maikaba kuma ya nada kwamitin bincike don tabbatar da laifuffukan daya zana masa.

Ba’a gama wannan hatsaniyar ba ta Little da Maikaba ba, sai Babangida Little kuma ya juya kan sakataren kwamitin gudanarwa kungiyar, Dokta Sani  Ibrahim. Inda ya jawo wani sakataren kuma ya kauda Dokta Sani.

Little ya kafawa  Dokta Sani kahon zuka wanda har sai da ya shawo kan sauran yan kwamitin gudanarwar kungiyar su goma sha daya suka rattaba hannu akan wata takarda data nuna rashin iya aiki na Docta Sani Ibrahim.

Wannan sa hannu dayan kwamitin sukayi akan rashin iya aikin da suka ce mutum mai digiri uku yayi ya ba kowa mamaki domin Little bai dauke yan kwamitin gudanarwar da mutunci da kima ba, kuma baya komai dasu. Don haka ta yaya suka yadda da sa hannu akan son zuciyar Little? Allah ma sani.

Ana cikin haka da Little ya kara bunkasa har ya kori sakataren hukumar Dokta Sani daga aikinsa na sakatare  duk da bashi ya nadashi ba.

Ana kuma zargin Little da kawo wani sakataren wanda gwamnati batasan dashi ba don son zuciya da kuma zargin sawa a balle mukulin ofishin Dokta Sani don kwasar wasu takardu da bayanai ba tare da sannin Dokta Sani ba.

Wannan a wata majiya tasa shi Dokta Sani rubuta takarda ga gwamnati don sanarda ita halinda da ake ciki.

Abin saurare shine, wane mataki gwamnati zata dauka akan shi Little domin ana zargin badakaloli da dama akansa.

Akwai bashishshika na miliyoyin nairori da Little ya amsa don cigaba da gudanar da kungiyar kafin a sakarwa kungiyarr kudin gudanarda ayyukanta a baya.

Akwai kudade masu yawa da kungiyyar ta ke samu wajen talloli da kuma shiga kallon wasanta a nan gida.

Koda zuwa  wasanni na waje yakamata gwamnati ta tuhumi yadda aka kashe Naira  miliyan 25 a wasannin uku na (Federation Cup) wanda akayi a Jos, Bauchi da Abuja.

Akwai kuma bukatar sanin yadda aka kashe Naira miliyan 18 a wasa daya na Pillars da kungiyar Abia Warrious.

A karshe zanyi kira ga gwamnati da nemi masana da kwararru wadanda muna dasu tinjim a jiharnan don shugabantar Kano Pillars da Sports Commission.

Yakamata gwamnati ta sani Allah yya albakarci Kano da malamai da masana harkokin wasanni a Kano kamarsu  Parfesa Rabiu Muhammad, Parfesa Musa Garba AA, Dr. Sani Ibrahim,  Dr. Bashir Maizare, Dr. Muhammda Musa da sauransu.

Idan aka hadasu da sauran mutanen gari  zasu kara habaka martabar Kano a farrnin wasannin.

Allah ya taimaka, ameen

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.