Nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar Kano karkashin limancin mai girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusif zata dunguzawa kungiyar kwallon kafa ta KanoPillars miliyoyin kudade, binciken wannan kafa ya bayyana.

Binciken ya nuna cewa gwamnatin jihar Kano na sane da irin mawuyacin hali da kungiyar kwallon kafar Kano Pillars ke fuskanta saboda rashin issassun kudade don gudanar da ayyukanta.

 “Gwamnati na sane da mawuyacin hali da kungiyar take ciki na rashin issassun kudade saboda gudanar da kungiyar,’’ cewar wani jami’in gwamnati wanda baiso a bayyana sunansa bas abo da rashin ikon yin hakan.

Haka kuma gwamnati na shirin dunguzawa kungiyar miliyoyin kudade don biyan dukkannin bashin da ake bin ta da kuma cigaba da gudanar da kungiyar.

“Haka kuma gwamnati na shirin dunguzawa lalitar kungiyar miliyoyin kudade don fitar da ita daga halin ni yasu da kungiyar ke ciki wanda ya dabai baye ta,’’ wata majiyar ta kara tabbatarwa.

Sai dai majiyar ta kara tabbatarwa wannan kafa yiyuwar yiwa mahukuntan kungiyar garanbawul ko kuma sauke su baki daya saboda rashin gamsuwa da yadda suke tafi da aikinsu.

“Gwamnati ta gano babbar matsala a tsakanin mahukuntan kungiyar Kano Pillars, a inda suke ta fadi-in-fada tsakaninsu , al,amarin da baya yiwa gwamnati dadi,” majiyarmu ta tabbatar.

Mamaye komai da shugaban kungiyar yayi da kuma rashin jawo dukkannin mambobin kungiyar jiki don ayi komai dasu baiyiwa gwamnati dadi ba, majiyar tamu ta kara bayyana mana.

Wannan tasa manya shiga tsakanin yan kwamitin gudanarwa da shugaban kwamitin gudanarwar sau da dama.

Ko dai menene gaskiyarr al’amari lokacine zai bayyana.

A cigaba da bibiyarmu don kara zakulo gaskiyar al’amari

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.