Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      Anya ba hakkin yan wasa da ma su horaswa ke bin Pillars, Barau ba?

      November 6, 2025

      NUGA Games: Northwest Varsity Departs, Poised for Excellence

      November 5, 2025

      Canjin shugabannin Kano Pillars: Ba shi bane mafita

      November 5, 2025

      Korar Yaro Yaro a Pillars: Menene laifin sa?

      November 3, 2025

      Dr. Maizare emerges VP, Karate Federation

      October 26, 2025
    • Column

      Fitness Test: Over 1,500 Referees, Assessors to converge in Kano ‘morrow

      November 7, 2025

      NPFL: Can Kano Pillars stand test of time?

      November 3, 2025

      TSY: Accomplished talent scout, content producer, football agent

      October 27, 2025

      NPFL’s unjust and unfair treatment for Kano Pillars

      October 20, 2025

      On Shehu Adamu’s assessment of Kano Pillars’ poor performance

      October 13, 2025
    • News & Media

      70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Ibrahim Shekarau

      November 5, 2025

      70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Shekarau

      November 5, 2025

      Happy birthday, Magistrate (Coach) Ibrahim Gwadabe

      November 3, 2025

      Kidney Patients send SOS to Governor AKY

      October 29, 2025

      Ganduje named Mi-Yetti Allah’s adviser for youth empowerment

      October 25, 2025
    • Analysis

      Matsalar Kano Pillars ibtala’ice, amma…

      October 28, 2025

      Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

      October 22, 2025

      Technical Advisor, Assistant for Kano Pillars Suspended: What’s next for Sai Masu Gida?

      October 21, 2025

      Korar Ogenye da Yaro Yaro: Ba su suka kar zomon ba

      October 20, 2025

      Rashin kokarin Kano Pillars da Barau: Sai fa gwamnati ta yi wani abu

      October 7, 2025
    • Personality Profiles

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024

      Engr. Ibrahim Usman Aikawa: New Kano Poly Governing Council’s PAB’s representative

      August 24, 2024

      Aminu Kano 40 years after…

      April 17, 2024

      Ameh Agnes: A woman farmer of repute

      April 15, 2024

      Dr. Usman Ibrahim Aikawa: New Kano Poly, Director Academic Planning

      January 2, 2024
    Sports Eye
    Home » Korar Yaro Yaro a Pillars: Menene laifin sa?
    Sports News

    Korar Yaro Yaro a Pillars: Menene laifin sa?

    Sani YusifBy Sani YusifNovember 3, 2025
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram
    1a

    Coach Ahmed Garba “Yaro Yaro” sanannan dan kwallon kafa ne a kasa Nigeria wanda yayi shura ya kuma bada taimako ainan a cigaaban kwallon kafa a matsayinsa na dan wasa da kuma a yanzu na mai horar da yan wasa.

    An haifi Yaro Yaro a 24 ga watan Mayu 1980 a jihar Kano, kuma ya fara wasan kwallon kafa tun yana yaro karami har izuwa girman sa.

    Yaro-Yaro ya fara buga was an kwallon kafa ne a ƙungiyar matasa ta Phyramid  kafin ya shiga ƙungiyar babban ƙungiyar.

    Wani sahihin bayani ya nuna cewa Yaro Yaro tun shekarar 1995 ya shiga babban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

    Kuma shi Yayo Yaro ya ta bugawa Kano Pillars wasa tun daga 1995 har izuwa 2001 wanda daga nanne ya sami tsallakawa kungiyar Club Africain ta kasar Tunis har zuwa 2002.

    Yaro Yaro ya komo gida Nigeria inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International  a Shekara 2003.

    Yaro Yaro ya kuma sake tsallakawa kasar waje a inda ya koma kungiyar Akademisk Boldklub dake Denmark a shekarar 2004 zuwa 2007’

    Daga baya ya komo gida Kano a inda ya cigaba da bugawa  kungiyar Kano Pillars wasa har zuwa lokacin daga bisani ya koma ƙungiyar Wikki Tourists.

    Yaro Yaro ya sami gayyata zuwa kungiyar kasa (Nigeria national football team) daga 1998 zuwa 2003.

    A cewar  shi Yaro-Yaro a shekarar 1997 aka nemeshi don zuwa ƙungiyar Borussia Dortmund II, a wata  yarjejeniyar shekaru huɗu, amma ƙungiyar Kano Pillars ta hana a kammala saboda yana ƙarami kuma ba a biya kungiyar Kanpo Pillars yadda ya dace ba.

    Tare da Yaro Yaro ne a shekarar 2008 kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta  lashe gasar ƙasa (league).

    Kuma an nadashi  matsayin babban mai horarwa (interim coach) na Kano Pillars  a shekarar 2017.

    Bayan yin ritaya daga wasa, sai Yaro Yaro ya tsunduma harkar horarda matasan yan wasa na kungiyar ta Kano Pillars.

    Tun daga shekarar 2015 zuwa 2017 har izuwa kwannan yana aiki da kungiyar Kano Pillars a matsayin mataimakin babban mai horaswa kafin kwananan a sallameshi.

    Wani abin tambaya shine menene laifin Yaro Yaro wanda yasa shugannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sallamarsa tare da babban mai horarwa Evans Ogenyi?

    A ganin mutane da dama daukar alhakinsa akayi domin bashi bane mai wuka da nama a kunginyar. Domin a matsayinsa na mataimaki, aikinsa shawara wanda ba kuma dole shi babban mai horaswa yayi amfani da it aba.

    Mutane da dama da na zanta dasu sun nuna rashin jin dadi da kuma rashin gamsuwa da wannan mummunan mataki da hukumar gudanarwar Kano Pillars ta dauka akan Yaro Yaro.

    Wasu naganin kamar daukan alhakinsa akayi domin shi shawarace kawai aikinsa wanda sai anga dama ayi aiki da shawararsa.

    Ra’ayin mutane da dama ya nuna  bai kamata laifin wani ya shafi wani ba idan har ma akwai laifin.  Domin matsalar Kano Pillars ba matsalar mai horaswa bace.

    Kowa yasan matsalar Kano Pillars matsalace ta rashin ingattattun da zakakuran yan wasa wanda ba laifin Evans da Yayo Yaro bane.

    Wasu kuma na ganin matsalar Kano Pillars ta ibtala’in wasa kwallon kafa ce wanda zata iya zowa ga  kowa da kowa duk kwarewa da iya wasan yan wasan shi..

    Gashi yanzu an kawu sabon mai hohoraswa kuma babu abinda ya canja a kungiyar.

    Game da wadannan bayanai, muna kira da babbar murya ga hukumar gudanarwar kungiyar karkashin shugabancin Muhammadu Ali Nayara Mai Samba da su dubi Allah su sake duba lamarin sallamar Yaro yaro da idon rahama don ya dawo kan aikinsa.

    Idan kuma an dawo dashi ayi kokarin turashi yin Kwas na Lasisin Mai horaswa na CAF Grade B don kara kwarewa akan aikinsa.

    Hakan zaisa idan ya dawo ya cigaba da bada gudunmawar da yake bayarwa don cigaban kungiyar.

    Yakamata mu zama masu gina mutanenmu, ba masu rugurguzasu ba. Ina kukeson yanzu shi Yaro Yaro ya koma tunda bai bude ido da yawace yawace ba?

    Allah yasa mu dace.

     

    A Pillars Korar Menen Yaro Yaro
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleNPFL: Can Kano Pillars stand test of time?
    Next Article Happy birthday, Magistrate (Coach) Ibrahim Gwadabe
    Sani Yusif
    • Website

    I was a staff of the then Triumph Newspapers, with keen interest in sports journalism which drove me to the unit where I was supported and oiled in the dynamics of modern sports reporting by my mentor/friend, Sani Zaria, the then Group Sports Editor of the Triumph. And when he left in 1995, I tried to sustain the spirit against all odds with a column sportesye. But when The Triumph was closed, I was moved to Kano Polytechnic as a lecturer until my retirement last 3 years, which gives me time to return to what I know best , the recreation of the SPORTS EYE.

    Related Posts

    Anya ba hakkin yan wasa da ma su horaswa ke bin Pillars, Barau ba?

    November 6, 2025

    NUGA Games: Northwest Varsity Departs, Poised for Excellence

    November 5, 2025

    Canjin shugabannin Kano Pillars: Ba shi bane mafita

    November 5, 2025

    Dr. Maizare emerges VP, Karate Federation

    October 26, 2025

    Dala Hard Courts Director elected VP, Nigeria Tennis Federation

    October 26, 2025

    Dala Hard Courts Director elected VP Nigeria Tennis Federation

    October 26, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    Fitness Test: Over 1,500 Referees, Assessors to converge in Kano ‘morrow

    November 7, 2025

    Anya ba hakkin yan wasa da ma su horaswa ke bin Pillars, Barau ba?

    November 6, 2025

    70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Ibrahim Shekarau

    November 5, 2025

    70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Shekarau

    November 5, 2025

    NUGA Games: Northwest Varsity Departs, Poised for Excellence

    November 5, 2025
    © 2025 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.