Gobe Jumaa ne dubunnan magoya bayan kungiyar wasan Kwallon Kafa ta Barcelona ta kasar Supaniya na jahar Kano zasu tattara a rufaffen dakin wasa na Kofar Mata dake Sani Abacha Complex don bikin murnar dimbin nasarorin da kungiyar tasu tayi a kakar wasan da ta gabata.
Su dai magoya bayan kungiyar karkashin shugabancin Bala Abi Doka na farin cikin dinbin nasarorin da kungiyar tasu ta samu a kakar wasanni na 2024–2025 a inda FC Barcelona ta sami nasarorin cin kofin wasannin cikin gida guda uku.
Na farko dai kungiyar tayi habzi da kasurgumin kofin La Liga (Spanish League)
Ita waccen nasara it ace ta 28 wajen cin kofin La Liga a karkashin coach Hansi Flick.
Nasara ta biyu ita ce ta lashe kofin Copa del Rey (Spanish Cup)
A 26 ga watan Afirilu, 2025, Barcelona ta sami nasarar cin wannan kofi na Copa del Rey wanda shine na 32 bayan ta lallasa Real Madrid 3–2 a filin wasa na La Cartuja a Seville.
Nasara ta uku kuwa it ace ta cinye kofin Supercopa de España (Spanish Super Cup)
Barcelona ta sami nasarar cin wannan kofin wanda shine na 15 bayan ta yiwa 5–2 Real Madrid dakan Sakwara da ci 5 da 2..
Haka kuma kungiyar ta Barcelona har sai da ta kai was an kusa da na karashe a gasar Champions league watau semi-finals a inda Inter Milan tayi waje da ita a extra time.
Wadannan nasarori da Barcelona ta samu ne yasa magoya bayan ta anan Kano karkarshin Shugancin Bala Abi Doka suka shirya taro do yin hamdala ga Mai duka, Allah SWT da kuma sada zumunci a tsakaninsu.
Ita dai kungiyar FC Barcelona ta Sapaniya an kafata a shekarar 1899 kuma sun fara wasan sada zumunci na farko ranar 8 December 1899.
Da farko dai kungiyar FC Barcelona ta fara da buga kananan wasanni a kasar ammama shekarar 1929 kungiyar ta zama daya daga cikin kungiyoyin da aka fara gasar La Liga da su.
Kuma ita FC Barcelona tana daya daga cikin kungiyoyin uku (Athletic Bilbao da Real Madrid) da basu taba dawowa ajin baya ba (religation) a tarihi ba.
Tarihi ya nuna daga 1919 zuwa 1929, Barça ta lashe kofin Copa del Rey sau biyar da kuma Campionat de Catalunya sau tara. Kuma FC Barcelona ta lashe kofina biyar a kakar wasa ta 1951–52.
A wani bayani da wannan kafa ta samu daga bayan fage, manyan mutane da mawakane zasu halarci waje.
Da fatan Allah yasa ayi taro lafiya a kuma gama lafiya. Ameen.