Coach Ahmed Garba “Yaro Yaro” sanannan dan kwallon kafa ne a kasa Nigeria wanda yayi shura ya kuma bada taimako ainan a cigaaban kwallon kafa a matsayinsa na dan wasa da kuma a yanzu na mai horar da yan wasa.
An haifi Yaro Yaro a 24 ga watan Mayu 1980 a jihar Kano, kuma ya fara wasan kwallon kafa tun yana yaro karami har izuwa girman sa.
Yaro-Yaro ya fara buga was an kwallon kafa ne a ƙungiyar matasa ta Phyramid kafin ya shiga ƙungiyar babban ƙungiyar.
Wani sahihin bayani ya nuna cewa Yaro Yaro tun shekarar 1995 ya shiga babban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.
Kuma shi Yayo Yaro ya ta bugawa Kano Pillars wasa tun daga 1995 har izuwa 2001 wanda daga nanne ya sami tsallakawa kungiyar Club Africain ta kasar Tunis har zuwa 2002.
Yaro Yaro ya komo gida Nigeria inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International a Shekara 2003.
Yaro Yaro ya kuma sake tsallakawa kasar waje a inda ya koma kungiyar Akademisk Boldklub dake Denmark a shekarar 2004 zuwa 2007’
Daga baya ya komo gida Kano a inda ya cigaba da bugawa kungiyar Kano Pillars wasa har zuwa lokacin daga bisani ya koma ƙungiyar Wikki Tourists.
Yaro Yaro ya sami gayyata zuwa kungiyar kasa (Nigeria national football team) daga 1998 zuwa 2003.
A cewar shi Yaro-Yaro a shekarar 1997 aka nemeshi don zuwa ƙungiyar Borussia Dortmund II, a wata yarjejeniyar shekaru huɗu, amma ƙungiyar Kano Pillars ta hana a kammala saboda yana ƙarami kuma ba a biya kungiyar Kanpo Pillars yadda ya dace ba.
Tare da Yaro Yaro ne a shekarar 2008 kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lashe gasar ƙasa (league).
Kuma an nadashi matsayin babban mai horarwa (interim coach) na Kano Pillars a shekarar 2017.
Bayan yin ritaya daga wasa, sai Yaro Yaro ya tsunduma harkar horarda matasan yan wasa na kungiyar ta Kano Pillars.
Tun daga shekarar 2015 zuwa 2017 har izuwa kwannan yana aiki da kungiyar Kano Pillars a matsayin mataimakin babban mai horaswa kafin kwananan a sallameshi.
Wani abin tambaya shine menene laifin Yaro Yaro wanda yasa shugannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sallamarsa tare da babban mai horarwa Evans Ogenyi?
A ganin mutane da dama daukar alhakinsa akayi domin bashi bane mai wuka da nama a kunginyar. Domin a matsayinsa na mataimaki, aikinsa shawara wanda ba kuma dole shi babban mai horaswa yayi amfani da it aba.
Mutane da dama da na zanta dasu sun nuna rashin jin dadi da kuma rashin gamsuwa da wannan mummunan mataki da hukumar gudanarwar Kano Pillars ta dauka akan Yaro Yaro.
Wasu naganin kamar daukan alhakinsa akayi domin shi shawarace kawai aikinsa wanda sai anga dama ayi aiki da shawararsa.
Ra’ayin mutane da dama ya nuna bai kamata laifin wani ya shafi wani ba idan har ma akwai laifin. Domin matsalar Kano Pillars ba matsalar mai horaswa bace.
Kowa yasan matsalar Kano Pillars matsalace ta rashin ingattattun da zakakuran yan wasa wanda ba laifin Evans da Yayo Yaro bane.
Wasu kuma na ganin matsalar Kano Pillars ta ibtala’in wasa kwallon kafa ce wanda zata iya zowa ga kowa da kowa duk kwarewa da iya wasan yan wasan shi..
Gashi yanzu an kawu sabon mai hohoraswa kuma babu abinda ya canja a kungiyar.
Game da wadannan bayanai, muna kira da babbar murya ga hukumar gudanarwar kungiyar karkashin shugabancin Muhammadu Ali Nayara Mai Samba da su dubi Allah su sake duba lamarin sallamar Yaro yaro da idon rahama don ya dawo kan aikinsa.
Idan kuma an dawo dashi ayi kokarin turashi yin Kwas na Lasisin Mai horaswa na CAF Grade B don kara kwarewa akan aikinsa.
Hakan zaisa idan ya dawo ya cigaba da bada gudunmawar da yake bayarwa don cigaban kungiyar.
Yakamata mu zama masu gina mutanenmu, ba masu rugurguzasu ba. Ina kukeson yanzu shi Yaro Yaro ya koma tunda bai bude ido da yawace yawace ba?
Allah yasa mu dace.
