Hajia Hauwa Isa Ibrahim ita ce mai rikon mikamin shugabancin Gidan Talbijin na Abubakar Rimi watau (ARTV Kano) kuma mace ta biyu a tarihin gidan talabijin din da ta rike wannan mukamin.
Mai girma gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya fara nada ta matsayin mataimakiyar babban manajar gidan talabijin din ARTV, Kafin ya amince zamanta mukaddashin shugaban gidan talabijin na ARTV watau (MD ARTV) din.
Kafin akai ta ARTV, Hajia Hauwa maaikaciyar gidan radiyon Nasara ce, wanda gushewarta a baro babban gibi saboda kokarinta, aiki tukuru da kuma hangen nesanta a wajen aikinta.
Tafiyarta zuwa ARTV maaikatan gidan Radiyo Nasara sunyi jimami mai yawa saboda rashin uwa,kawa da kuma abokiyar aiki mara kyamar mutane, mara mugunta da kuma kaunar abokan aikinta.
Hajia Huwa mace mai girmama mutane da kuma hangen nesa wadda ta dare mukamin shugabancin ARTV ne bayan gushewar tsohon shugaban gidan talabijin din wasu lokutan baya.
Amincewa da mai girma gmamna yayi da nadin nata na zama mai rikon mikamin shugabancin gidan talabijin na ARTV, bai bawa mutane mamaki ba domin sanin cewa ansan zata iya daukar nauyin aikin da aka bata.
Haka kuma sanin kowane cewa kafin kasancewarta jagoriyar gidan ARTV din, gidan talabijin din nada ko fuskantar matsalolin da suka taru suka kassara gidan kuma suka hana gidan motsi wanda ya mayarda shi baya.
Amma darewar Hajia hauwa kan karagar jagorancin gidan keda wuya, Hajiyar tayi nasarar magance wasu daga cikin manyan matsaloliin gidan, wanda ya kawo tagomashi da kuma farfado dashi daga baccin daya shekara da shekaru yanayi.
Aikin tukuru da Hajiya Hauwa ta keyiwa gidan ARTV din yasa jamaa da dama dawowa kallo da kuma karin masu kallon shirye-shiryen gidan talabijin din.
Rashin sakankancewar Hajiyar ya sa ta aiki ba dare ba rana don tabbatar da kawar da tarin matsalolin da suka dabaibaye gidan talabijin din na ARTV mai tarin tarihi.
Sai dai samun taimakon Allah (SWT) da kuma amincewar mai girma gwamna da yakeyi mata wajen sahalewar dukkannin bukatunta na gyara, Hajia Hauwa ta sami nasarori da dama wajen shawo kan wasu daga cikin manyan matsalolin ARTV din.
Cikin nasarorin da Hajiyar ta samu sun hada da mayarda gidan talabijin na ARTV yin aiki awa 24 kullum ba kamar yadda yake da ba.
Hajiar tayi nasarar dora shirye-shiryen gidan talbijin din gabadayansu kan Tauraron Dan Adam na NAGCOMSAT, wanda yasa a halinn yanzu gidan talabijin ARTV ana kallon shirye-shiryensa a duk duniya.
Hajiyar da kuma inganta ayyukan gidan wajen samarda kayan aiki na zamani a kowane farni ko bangare na gidan ARTV din.
Hajiyar kuma tana ta kokarin horar da maaikatan gidan iya sarrafa sababbin na’urorin da ta samar a gidan.
Ba kamar da ba, yanzu Hajiyar ta gyara na’urorin bada wuta wanda yasa gidan talabijindin ke aiki ko ba wutar NEPA safe da rana.
Hajiyar kuma ta fara shirin samawa maaikatan gidan talabijin din horo don kara kwarewa da sanin makamar aiki.
Don muji yadda mutanen gari da kuma abokan aikinta suke ganin wannan cigaba da takawo, www.sportseye.ng ta zagaya don jin raayin mutane akan yadda suke ko suka ga kokarin Hajia Hauwa Isa Ibrahim akan wannan kujera.
Hafsat Sani Muhammad, tsohowar shugabar kungiyar mata yan jarida ta Kano watau NAWOJ
A gaskiya na yaba da kuma jinjinawa kokari da hazakar Hajiya Hauwa wajen ganin ta canja akalar gidan talabijin din ARTV.
Hakika kasancewar Hajia Hauwa jagoriyar ARTV ya zama alheri domin tarin alherin da ta kawowa gidan da maaikatan gidan baki daya.
Nasarorin da ta samu yasa gidan talbijin na ARTV da dukkan maaikatan gidan alfahari da kuma murnar shugabancin Hajia Hauwa saboda tarin cigaban da ta kawowa gidan talabijin din.
Duk munsan tarin matsaloli da ARTV ke dda shi lokacin da Hajia Hauwa ta zama jagorar gidan, amma fa yanzu duk sun zama tarihi domin ta samawa gidan talbijin na ARTV kayan aiki na zamani masu tarin yawa kuma a kowane farni ko sashe na gidan.
A ganina dole ne a gode da kuma yabawa mai girman gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf saboda zakulo zakakurar mace irin Hajiya Hauwa da kuma damka mata shugabancin gidan ARTV, wanda ko kusa bata bawa mara da kunya ba.
Wannan tasa ya zama dole mu yaba masa saboda gudummawar da yake bata wajen sahalewa da amincewa dukkannin bukatun da ta mikawa ofishinsa.
Haka kuma dole a yabawa ita Hajia Hauwa bisa kokarinta na horar da maaikatan gidan talabijidin ARTV don kara sanin makamar aiki da kuma kwarewa da sannin yadda za suyi amfani da dukkan naurorin aiki na zamani da shugabancinta ya samar.
Aisha Miqdad, shugabar ashen mata da kananan yara na radiyon Nasara
Ni nasan Hajia Hauwa Isa Ibrahim sosai. Macece aminiyar kowa, kuma mai haba-haba da kowa ga kokari ga aiki tukuruu ga kuma rufawa masu aiki a karkashinta asiri.
Ba tada boye-boye kuma aikin kawai ta sa a gaba. Na yabawa mai girma gwamna daya bata wannan aiki domiin na da tsofaffinn abokan aikinta munsan bazata bamu kunya ba.
Gashinan kowa yana ganin aikinta a zahiri domin kowa yabawa kkokarinta kawai yake tayi. Dama munsan zata iya kuma gashin ana gani.
Fatanmu da addu’armu shine ta kara kokari kada ta baiwa maigirma gwamna kunya bisa ga amanarda daya bata.
Murtala Sale Fagge, Mai Itace
A gaskiya kasancewar wannan baiwar Allah jagoriyar wannan gida wanda mukafi da sunan CTV67 a da, wanda a halin yanzu ake kira ARTV ansami cigaba mai tarin yawa.
Hakika Hajiya Hauwa ta baiwa mara da kunya domin tayi abinda da yawa suka kasa a baya.
A ganina, ganin shirye-shiryen gidan talabijin din safe, rana da daddare ba karamin cigaba bane kuma abin alfaharine.
Ina yabawa maai girma gwamna Abba Kabir Yusuf saboda nasarar samo abokiyar aiki. Hakika ita Hajiya macece mai kamar maza…
Muhammadu Wasilu Kawo, shugaban sashen wasanni na gidan radiyon Nasara
Aganina baiwa Hajia Hauwa aikin mai wuya irin wannan wanda mai girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf yayi, abune wanda ya dace saboda sanin kokarinta da jajircewarta wajen aiki da sanin yakamata.
A lokacin muke aiki tare a gidan radiyo Nasara, musan Hajiya Hauwa da tsari da kuma aiki tukuro don haka bata wannan mukami abune a hangenmu wanda ya dace.
A gidan Radiyo Nasara mun san irin kokarinta, juriyarta da hazakarta wajen aiki, don haka cigaban da muke gani yau a ARTV bai bamu mamaki ba.
Addu’armu Allah ya cigaba da taimakawa kokarinta, ameen.