Dare warsa gadon mulkin karamar hukumar Fagge keda wuya, sabon shugaban karamar hukumar Fagge, Hon. Salisu Masu ya bayyana rushe dukkannin sassuna sama da 40 da ake karbar kudin shigar karamar hukumar baki dayansu.
Ayyana rushe masu karbar kudin shigar na karamar hukumar, sai komi ya tsaya cak inda shigar kudi aljihun karamar hukumar ya tsaya shima cak.
Bincike ya nuna cewa dakatar da masu karbar kudin shigar karamar hukumar yin aikinsu yasa karamar hukumar asarar miliyoyin nairori.
Mutane da yawa da muka zanta dasu sun nuna mamakin yin hakan domin daga lokacin da shugaba Masu ya ayyana dakatarwar zuwa yau kusan wata guda kenan, kuma yakamata ace duk abinada zai kawo tsaikon sake sababbin masu tattara kudin shiga a kauce masa.
Wata majiyar ta nuna cewa tsaikon nada sababbin masu tattara kudin shigar ya samune saboda matsin lamba da wasu keyi akan aba damar tattara kudin da kuma inda suke so a tura su.
Wata majiyar kuma ta nuna shaawar wasu manyan jigajigen siyasar Fagge game da tattara kudin shigar don samawa mabiyansu madafa.
Koma me ake ciki yakamata shugabannin karamar hukumar su farka domin dakatar da sulalewar ko asarar miliyoyin kudin shiga.