“Anya kuwa ba alhakin wasu yan wasa da masu horar da yan wasan ke bin kungiyoyin Kano Pillars da Barau dake cikin gasar pirimiya ta kasa watau NPFL ke bin suba?”
Wannan tambayar kuma mai wuyar amsawa ta biyo baya ne saboda ganin yadda kungiyoyin biyu watau Pillars da Barau suka kasa tabika wani abin azo a gani tun farko kakar wasa ta bana zuwa wannan lokacin.
Duk da kowa yasan cewa da kungiyar Kano Pillars da ta Barau din babu mai wata matsalar kudi ko kayan aiki, amma sun kasa komai a wannan kakar wasan ta bana. Duk da suna taka waSa iya gwargwado ko karfinsu.
Domin kwana kwanannan gwamnatin jihar Kano ta gwangwaje kungiyar Kano Pillars da sabbabbin motoci don sawwake musu wahalar tafiye tafiyen zuwa wasansu na waje.
Ita kuma kungiyar Barau a jirgin sama suke kai yan wasansu zuwa wasansu na waje don rage ko kawar musu da gajiyar dogowar tafiya mai nisa.
Bincike ya nuna cewa yan wasa da yawa da kuma masu horaswa (coaches) na dukkanin kungiyoyin biyu watau Pillars da Barau nada wani hakki a tare da kungiyoyin biyu wanda shine ke bin kungiyoyin.
Wannan ta sa aka fara danganta rashin nasara ko tabika wani abin azo a gani na kungiyoyin biyu a gasar pirimiya wadda wannan makon take shiga makonta na goma.
Binciken ya kuma nuna cewa cin zarafi da kungiyoyin biyu suka yiwa masu horasda yan wasansu (coaches) a baya ba zai barsu suyi wani abin kirki a gasar ba.
A bangaren Kano Pillars anga yadda mahukuntan kungiyar tare da hadinkan wasu magoyabaya kungiyar suka sa masu horaswa biyu kamar Audu Maikaba da Usman Abdallah a gaba wanda har saida akaga bayansu.
Bincike ya sake nuna yadda masu horaswar biyu suka bar kungiyar ba dan suna so ba, saidai dan babu yadda za suyi.
A bangaren yan wasa kuwa, akwai labarin fifita wasu yan wasan akan wasu saboda kawai su yaran wani ko wasu daga cikin shugabannin kungiyarne.
Akwai rade-radin cewa idan dan wasa bashi da tagomashin wani ko wasu daga cikin shugabannin Kano Pillars ko magoyabayansu to sam bazai kai labara ba duk kyau ko kokarinsa.
Koshima mai horaswa da kungiyar Kano Pillars ta kora baya-bayannan watau Evans Ogenyi mutane da dama suna ganin baa kyauta masa ba domin baa bashi damar kare kansa ba.
A bangaren kungiyar Barau kuwa, kowa yaga yadda Rabiu Tata yayi kokari ba dare ba rana yakai kungiyar matakin da take akai yau, amma meya faru? Sai kawai aka kakaba masa wani daga sama wai a sunnan babban mai horaswa.
Ha kuma bincike ya nuna cewa yawancin yan wasan da suka sha wahalar kai kungiyar Barau matakinta na yanzu, abin haushi anyi watsi dasu kuma babu wani tagomashi da akayi musu don nuna godiya da kokarinsu.
A bangaren Barau dindai, akwai zargin cinzalin yan wasa da yawa wanda su kadai baza su bar kungiyar Barau din taka wata rawar kirki ba.
Zargi na farko wanda ake ganin alhakinsa zai iya nisanta kungiyar Barau daga nasara shine wanda aka salami yan wasa ba tare da gode musu da kuma basu hakkokinsuba.
Zargi na biyu shine hana wasu yan wasan kyautar Babura daya-daya da Sanata Barau Jibrin Maliya ya basu bayan samun nasarar kai kungiyar gasar pirimiya ta kasa.
Wannan ta faru ne domin wasu ba a basu baburar kamar yadda shi sanata Barau yace a bada ba. Ance wasu an basu amma wasu mutum biyu-biyu ko sama da haka aka hada aka bawa.
Haka kuma ana zargin yiwa yan wasan kungiyar Barau gaftare da gibin albashinsu ko kuma wata kyautar kudi da Sanata Barau ya bada don a rabawa yan wasan kungiyar wanda yakamata sanata yasa abincika.
Wadannan da wasu zarge-zargen sune wasu daga cikin ahakin yan wasa dana cin zarafin masu horaswa wanda ke bin kungiyoyin Kano Pillars dana Barau .
A ganina yakamata baa makaraab, a duba idan an tabbatar to akirawosu a basu hakuri don kungiyoyin biyu su cigaba da samun tagomashi.
