Hakika babu laifi idan dan kwallo ko wani mutu yayi wani abu ko yabi wata hanya da zata bunkasa rayuwarsa.
Saboda bin hanya ko tafarkin bunkasa rayuwa abune mai kyau saboda amfanin da zaa samu a bayan anci nasarar samun abinda ake nema.
Saidai yakamata ko kuma ya zama dole abi a hankali ko kuma a lura sosai kafin yanke shawarar tafiya neman harkar bunkasa rayuwar.
A halin yau, yan wasan kwallon kafa da dama nata yunkurin fita kasashen waje inda sana’ar kwallon kafa keda bunkasa da room mai yawan gaske.
Amma kash, mafi yawancinsu na tsallakawa kasashen waje babu kyakkyawan shiri da tsari wanda yake jefasu cikin haliin ni yasu.
Yakamata kamin dan wasa ya fara tunanin tsallakawa ya tabbatar yakware kuma yasan kungiyar da zashi kuma suma sun sanshi. Watau ya tura musu (profile) dinsa da kuma wasu wasannin da ya buga don susan da zuwansa.
Tafiya kai tsaye neman kungiyar da zaiyi wasa a ciki kuskurene. Saboda zaijene a dan gwaji (trial) wand aba dole ne yayi musu yadda suke so ba.
Yakamata kafin tafiya bayan ya tabbatar ansan da zuwansa, yayi addua da sadaka da kuma neman albarkar iyaye da adduarsu.
Idan kunne yaji…