Kwanaki kadan da suka wuce  da rana tsaka, nayi kicibis da Ali Nayara Mai Samba, sabon shugaban hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Hakan ta faru ne ina zaune da wusu mutane a kofar gidana dake Kurna Asabe muna tattauna lamarin rayuwa.

Kwatsam sai naji sallama ta gefen hagu na. Amma kafin na juya naga mai yin sallama sai na amsa kuma sannan na juya don naga mai yin sallamar.

Duba me yimin sallama keda wuya sai naga ashe Alhaji Ali Nayara Mai Samba tare da wani dan makwabcina wanda ake kira Baban Hajiya suka kawomin ziyara don mu gaisa.

Nan take na tashi na tarbeshi na kuma mika masa hannu amma dukkanninsu suka nuke suka ki yin misabahar dani don girmamawa.

Bayan mun gaisa sai nayi masa murnar samun matsayin shugabancin hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, na kuma masa adduar fatan alheri, nasara da kuma gamawa lafiya.

Da Ali Mai Samba ya bude bakinsa sai nima ya godemin kuma ya nemine dana cigaba da bashi shawarwari don yin nasara da kuma cigaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Kafin ya juya ya tafi sai na nuna masa kalu balen dake gabansa da kuma yadda yakamata yayi don yakai labara.

Abu na farko dana fada masa shine ya dage ya zauna da yan kwamitinsa goma sha uku lafiya. Yayi amfani da darrasan da ya koya wajen rusasshen shugabancin hukumar baya wanda shima daya daga cikinsu ne.

Ka da ya sake ya dauki matsayinsa na shugaba yafi kowa a cikinsu. A’a ya daukesu abokan aiki domin tare aka nadasu kuma tare za suyi aiki na gudanarwa da kuma cigaban Kano Pillars.

Na fada masa ya rinka kiran yan kwamitinsa taro a duk lokacin da wata matsala ta taso don jin abinda ke bakinsu. Kuma kada ya rinka daukar mataki ko matsaya kai tsaye ba tare da jin ta bakinsu ba.

Na kuma bashi shawarar kafa kwamitin kwararru ((Technical Committee) don yin aiki tareda masu horar da yan was an kungiyar.

Anan ne  nace masa zai iya zabo masana wadanda suka kware ya hada da wasu daga cikin yan kwamitinsa don kasancewa yan kwamitin kwararrun.

Na uku na fada masa cewa ya lura da yadda ake daukar yan wasa a Kano Pillars kuma ya kawo masalaha wadda zata taimakawa Kano Pillars kuma ta taimakawa gwamnati.

Ta daukar yan wasa nata na kanta kawai kungiyar Kano Pillars zata iya rike kanta kuma ta samawa gwamnati manyan kudade a matsayin kudin shiga a duk lokacin  da zata sayarda dan wasanta ga wata kungiya ko gida ko waje.   

Na bawa Mai Samba shawarar dakatar da daukar danwasa ko yan wasa na zango daya daga (Agent(s)). Domin ana cutar kungiyar da kuma gwamnati sosai ta wannan bigiren. Na bashi shawarar daukan dan wasa ko yan wasa shekara biyu ko uku.

Domin ta hakane kawai kungiyar da kuma gwamnatin jihar Kano zasu amfana da kudi masu yawa a duk lokacin da wani dan wasan zai canja sheka zuwa wata kungiyar.

Na kuma  bashi shawarar zama lafiya da kungiyar magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars. Na fada mahimmancinsu da kuma yi masa nasihar mutuntasu da kuma  daukarsu abokan aiki.

Ya daukesu abokan aiki kuma ya rinka tuntubarsu lokaci-lokaci don sanin matsalolinsu da kuma taimaka musu sharesu.

 Na nuna masa  amfani da kuma tasirinsu musamman wajen bada goyon bayan da ake so a duk lokacin da Kano Pillars ke wasa gida ko waje.

Game da mutanenmu yan jarida kuwa na fadawa Mai Samba da suma ya kula dasu da muradunsu. Kada ya bare ya samu matsala dasu.

Na masa murnar samun mutum biyu a cikin kwamitinsa wadanda aka cemin dukkanninsu kwararrun yan jaridane da kuma bashi shawarar saurararsu don samun daidaito da abokan aikinsu.

Sai na sake  masa fatan alheri ya juya suka tafi.

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.

One thought on “Kicibis da Mai  Samba: Abubuwan da na fada masa”

Comments are closed.