A cikin wasanni hudu masu maki uku-uku wadanda idan aka tattara sun zama goma sha biyu da Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars ta buga a gida da waje a baya, kungiyar tayi barin maki goma.
Wane bincike da wannan mujallar ta gabatar ya nuna cewa Kungiyar Kano Pillars tayi barin maki goma daga cikin maki goma sha biyu al’amarin da ya sa kungiyar baro matsayi na uku da dake zuwa kasa a tebirin wasan kwaraarru na kasa.
Samun maki biyu kacal da kungiyar Kano Pillars tayi daga maki sha biyu shi ya haifar mata rasa wancan matsayi ko ma wuce shi.
Matsalar ta faru ne tun daga wasn kungiyar a jihar Katsina inda tayi rashin nasara da ci 2 da 3.
Dawowar kungiyar gida kuma sai tayi rashin nasara a wasanta da kungiyar Abia Warious da ci daya mai ban haushi.
Zuwan kungiyar Kano Pillars jihar Rivers anan ma sai tayi kunnen doki daya daya da masu masaukinsu.
Da kungiyar ta dawo gida sai ta sakeyin kunnen doki da kungiyar Enugu Rangers.
Hakika wannan rashin cikakkiyar nasara na kungiyar Kano Pillars da tayi a wasanni hudu a jere, ya jawo mata koma baya.
Anan zanyi kira da mahukumantan kungiyar da suyi binciken abinda ya jawo hakan don magancesu da wuri.
Su tuna yanzu ne lokacin jajircewa domiin an taho gangara. Hausawa na cewa, Aski idan ya taho goshi…